'Yan Bindiga Sun Kunyata, Sun Nemi Ba Sojoji Cin Hancin N2m a Jihar Taraba

'Yan Bindiga Sun Kunyata, Sun Nemi Ba Sojoji Cin Hancin N2m a Jihar Taraba

  • Rundunar sojin Najeriya ta kama masu garkuwa da mutane shida a yankunan ƙananan hukumomin jihar Taraba
  • Rundunar ta sanar da cewa an kama masu garkuwa da mutanen ne a kauyukan karamar hukumar Wukari da kuma Ibi
  • Ta kuma bayyana yadda jami'an ta suka ki karbar cin hanci da masu garkuwa da mutanen suka bayar domin a sake su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Whirl Stroke ta kama masu garkuwa da mutane shida a jihar Taraba.

Taraba
Sojoji sun kama yan bindigar da suka fitini jihar Taraba. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Ana zargin masu garkuwa da mutanen da aikata ayyukan ta'addanci a yankuna da dama a fadin jihar.

Rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook cewa a ranar 19 da watan Mayu ne dakarunta suka kama 'yan ta'addar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fatattaki mutane daga gidajensu a jihar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama 'yan bindiga a Wukari

Rundunar sojin ta samu bayanan sirri kan ayyukan da yan bindiga ke gudanarwa a kauyen Chinkai da ke Wukari.

Bayan kai samame yankunan jami'an soji sun kama Usman Gide da Abdulrahman Amadu wadanda dama suna cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.

'Yan bindiga sun ba sojoji cin hanci

A lokacin da sojojin suka kama masu garkuwa da mutane, sun yi kokarin ba su cin hancin N2m domin a sake su.

Amma sai sojojin suka ki karbar cin hancin domin nuna kishin kasa da kokarin dakile ayyukan ta'addancin ko ta halin kaka.

An kama yan bindiga a Ibi

A wani samamen da rundunar sojin ta kai garin Sarkin Kudu da ke karamar hukumar Ibi ta kama masu garkuwa da mutane hudu.

Masu garkuwa da mutanen da ake zargi sun hada da Jafaru Banyi, Mohammed Ardo, Amadu Lawal Shatta da Biyu Ardu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'in kwastam a Abuja

'Yan bindigar ake zargi da kama wasu 'yan Najeriya da ma yan kasashen waje suna karbar kudin fansa a jihar Taraba.

Sojoji sun kama 'yan bindiga a Kweserti

A wani rahoton, kun ji cewa sojoji da ke atisayen 'Whirl stroke' a jihar Taraba sun samu nasarar dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Kweserti da ke Ussa.

A yayin dakile harin ne sojojin suka yi nasarar kashe 'yan bindiga biyu tare da kwato makamai da harsasai yayin da 'yan ta'addan suka tsere.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel