An Samu Wanda Ya Ajiye Mukami Tun Kafin Tinubu Ya Sallami Shugabannin Hukumomi

An Samu Wanda Ya Ajiye Mukami Tun Kafin Tinubu Ya Sallami Shugabannin Hukumomi

  • Abubakar Adamu Rasheed ya bar kujerar da ya ke kai ta NUC mai kula da jami’o’in Najeriya
  • Shugaban hukumar ya rubuta takardar murabus, amma bai yi bayanin dalilin ajiye aikin ba
  • Farfesa Abubakar Rasheed wanda aka nada a lokacin Muhammadu Buhari zai koma aji

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban hukumar NUC mai kula da jami’o’i a Najeriya, Abubakar Adamu Rasheed ya sauka daga matsayin da yake kai a yanzu.

Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya sanar da cewa ya rubuta murabus da kan shi domin barin matsayin da ya yi shekaru har bakwai a kai.

Guardian ta ce Farfesan harshen Ingilishin ya shaidawa manema labarai wannan ranar Litinin a Abuja, ya nuna kwanakinsa sun zo karshe.

Shugaban Hukumar NUC
Shugaban NUC, Abubakar Adamu Rasheed Hoto: www.nuc.edu.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da Ake Zargi Ya Sace N70bn Ya Rabawa Mutane Goron Sallar N200m

Menene aikin NUC a Najeriya

Da yake yi wa ‘yan jarida bayani dazu, Abubakar Rasheed ya shaida cewa zai koma aji domin ya cigaba da koyarwar da ya bari a shekarun baya.

A dokar kasa, hukumar NUC ce ta ke kula da jami’o’in da ake da su a Najeriya, ita ce ta ke da damar bada lasisi da kuma karbe lasisi tun a 1972.

Punch ta ce a lokacin Rasheed ya na rike da hukumar ne aka samu karin sababbin jami’o’in ‘yan kasuwa, abin da ya bayyana a matsayin cigaba.

Rasheed ya bi sahun Jega

Kamar dai tsohon mai gidansa, Farfesa Attahiru A. Jega, Rasheed zai cigaba da karantar da daliban harshen Ingilishi a jami’ar Bayero da ke Kano.

Farfesan ya fara zama mataimakin shugaban jami’a ne, bayan an nada Jega a matsayin shugaban hukumar zabe, sai shi ya karbi ragamar a 2010.

Legit.ng Hausa ta fahimci Rasheed ya fara karantarwa ne a jami’ar ta Kano kusan shekaru 42 da su ka wuce, sai Farfesa ya kai shekara 70 yake ritaya.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Haɗu da Shugaban Kasar Benin, Ya Taɓo Batun Iyakoki da Kasuwanci

Shekaru 7 a NUC

A rana daya aka nada shugaban NUC tare da irinsu Bappa Aliyu, Abdullahi Baffa Bichi, Garba D. Azare, Micheal Afolabi, Ishaq Oloyede da Steven Onah.

Idan za a tuna, Adamu Adamu ne ya nada Chinyere Ohiri-Anichie duk a lokacin ya na Ministan ilmin tarayya, an yi haka ne tun a watan Agustan 2016.

Duk da ya na da ragowar shekaru uku, Farfesa Rasheed ya zabi ya ajiye aikin da kan shi.

Cire tallafin man fetur

Bincike da aka yi ya nuna APC ba za ta kai labari a zaben 2023 idan fetur ya tashi ba, rahoto ya zo cewa saboda tsoron rasa mulki aka bar tallafin mai.

Garba Shehu yake cewa a wani jawabi, maganar gaskiya dole Muhammadu Buhari ya yi abin da zai ba Jam’iyyar APC nasara, ka da a kunyata a zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng