Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Alhazan Najeriya 2 Suka Mutu a Saudiyya Yayin Aikin Hajjin 2023

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Alhazan Najeriya 2 Suka Mutu a Saudiyya Yayin Aikin Hajjin 2023

  • Alhazan Najeriya shida sun rasu yayin da suke aikin hajjin 2023 a garin Makkah, kasar Saudiyya, kamar yadda hukumar NAHCON ta sanar
  • Usman Galadima, shugaban tawagar likitocin NAHCON ya yi kira ga karfafa shirin tantance alhazai kafin tafiya aikin hajji domin magance yawan mace-mace
  • Tawagar likitocin sun kuma ce an samu masu lalurar tabin hankali, zubewar ciki da karayar kashi tsakanin tsoffin mahajjata

Saudiyya - Rahotanni daga Hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) sun bayyana cewa alhazan Najeriya shida da ke aikin hajji a bana sun mutu a kasar Saudiyya.

Shugaban tawagar likitoci na NAHCON a hajjin 2023, Usman Galadima ne ya bayyana haka a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, yayin wani taron hukumar a garin Makkah, Premium Times ta rahoto.

Aikin hajji
Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Alhazan Najeriya 2 Suka Mutu a Saudiyya Yayin Aikin Hajjin 2023 Hoto: Ashraf Amra/Anadolu Agency, Firat Tasdemir/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

A jawabinsa, Mista Galadima ya ce an samu mutane bibbiyu da suka mutu a tawagar alhazan jihohin Osun da Kaduna, yayin da aka rasa mutum daya a jihar Filato.

Kara karanta wannan

Babban Sallah: Sanata AbdulAziz Yari Ya Yi Wa Wasu Zamfarawa Tagomashin Alkhairi

Galadima ya yi kira ga karfafa shirin tantance mahajjata kafin tafiya aikin hajji

Domin magance yawan mace-mace, Mista Galadima ya yi kira ga karfafa shirin tantance lafiyar mahajjata kafin tafiya aikin hajji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewar akwai bukatar hana wadanda ake ganin basu da isasshen lafiya zuwa aikin hajji.

Da yake ci gaba da jawabi, ya kara da cewar tawagar likitocin sun kuma gano marasa lafiya 30 da ke fama da lalurar tabin hankali inda suke samun kulawa a yanzu haka kuma ana sa ran za su yi aikin hajji.

Mista Galadima ya ce:

"Muna ta kula da su a cibiyoyinmu. Muna da masu lalurar tabin hankali kimanin su hudu a tawagar. Muna ta kula da su kuma akwai yiwuwar dukkansu za su yi aikin hajji saboda sun dan daidaita yanzu."

Jami'an sun kuma bayyana cewa an samu mata biyu da suka yi barin ciki yayin da suka karbi haihuwar mace daya, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi

Ya ce:

"An haifi daya daga cikin yaran ta hanyar tiyata - cikin watanni bakwai ne."

Ya bayyana cewa an yankewa daya daga cikin marasa lafiyan wani bangare na jiki saboda ciwon siga. Baya ga wanda aka yankewa sassa, Mista Galadima ya kuma ce tawagar sun damu dangane da yawan karaya da ake samu tsakanin tsoffin mahajjata.

Ya ce tawagar ta samu mutane takwas da suka karye.

Hajjin 2023: Gwamna Uzodimma Ya Dauki Nauyin Mahajjata 200

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya kaddamar da shirin zuwa Makkah, kasar Saudiyya ga maniyyata a jihar domin aikin hajjin 2023.

Da yake jawabi a gidan gwamnatin jihar da ke Owerri, Gwamna Uzodimma ya bukaci Musulmai 200 da za su aikin Hajji a jihar da su zamo jakadun kirki na jihar sannan su nuna dabi'ar kwarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel