Bikin Babban Sallah: Sanata Yari Ya Gwangwaje Makwabtansa Da Raguna 500

Bikin Babban Sallah: Sanata Yari Ya Gwangwaje Makwabtansa Da Raguna 500

  • Sanata Abdul’aziz Yari ya rabawa makwabtansa, marasa gata, da yan gudun hijira raguna 500 domin su yi bikin babban sallah a karamar hukumar Talata-Mafara
  • Wannan kari ne a kan raguna 1,000 da shanaye 400 da tsohon gwamnan na zamfara ya rabawa jiga-jigan APC a jihar
  • Nan da yan kwanaki daukaci al'ummar Musulmi za su yi bikin babban sallah inda ake yanka raguna da sauransu domin layya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Zamfara - Sanata Abdul’aziz Yari, mai wakiltan Zamfara ta yamma, ya rabawa makwabtansa da marasa karfi a garin Talata-Mafara da ke karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar raguna 500 domin su yi bikin babban sallah.

Shugaban kwamitin rabon, Alhaji Sha’aya Sarkin-Fawa ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da ragunan ga wadanda suka ci moriyar shirin a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Nada Kwamiti, Za a Binciki Shekaru 4 da Tsohon Gwamna Ya Yi

Sanata AbdulAziz Yari
Bikin Babban Sallah: Sanata Yari Ya Gwangwaje Makwabtansa Da Raguna 500 Hoto: @AbdulazizY22602
Asali: Twitter

Da farko ya rabawa jiga-jigan APC a Zamfara raguna 1,000 da shanaye 400

Sarkin-Fawa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kun sani, wannan karamci ne da shugabanmu, Sanata Yari ya saba yi duk shekara domin taimakawa marasa karfi don su samu damar yin bikin babban sallah cikin sauki.
“Wannan na makwabtansa, marasa karfi, yan gudun hijira da marayu a garin Talata-Mafara ne kawai.
“Wannan kari ne a kan raguna 1,000 da shanaye 400 da ya raba da farko ga jagororin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matakan jihar, karamar hukuma da gudunmomi ta kungiyar siyasarsa."

Sarkin-Fawa, wanda ya kasance jigon jam’iyyar APC a jihar ya yaba ma tsohon gwamnan na Zamfara kan shirye-shiryensa daban-daban na tallafawa mutane a matakin farko.

Yay i kira ga Musulmai da su yi amfani da bikin babban sallah domin yi wa jihar da Najeriya addu’an samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

An Ba Abba Gida-Gida Wa’adin Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano, Cikakken Bayani

Gwamnatin Kano ta ba dalibai mako guda a matsayin hutun babban sallah

A wani labarin, mun ji cewa ga'aikatar ilimi na jihar Kano ta amince da Juna'a, 23 ga watan Yuni, a matsayin ranar fara hutun bikin babban sallah ga dukkanin makarantun jeka ka dawo da na kwana a jihar.

Bikin babban sallan wanda zai shafe tsawon mako guda zai kare a ranar Asabar, 1 ga watan Yuni.

Saboda haka, ana sa ran daukacin daliban makarantun za su dawo makaranta a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni yayin da masu jeka ka dawo za su koma a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel