Kwastam Ta Shammaci Wata Mota Makare Da Buhuna 414 Na Fatu Da Naman Jakuna, Ta Mika Su Ga Wata Hukuma

Kwastam Ta Shammaci Wata Mota Makare Da Buhuna 414 Na Fatu Da Naman Jakuna, Ta Mika Su Ga Wata Hukuma

  • Hukumar Kwastam reshen jihar Kebbi ta yi nasarar kama babbar mota makare da fatu da kuma naman jaki a iyakar jihar Kebbi
  • Hukumar ta kuma mika wadannan kayayyaki da ta kwace ga Hukumar Kula da Amfanin Gona (NAQS) don daukar mataki na gaba
  • A watan Mayu ne hukumar ta kama wasu mutane dauke da buhunan fatun da naman jaki guda 414 a iyakar jihar suna kokarin tsallakawa kasashen ketare

Jihar Kebbi - Hukumar Kwastam reshen jihar Kebbi ta kama wasu masu kokarin tsallaka Najeriya da buhunan fatu da kuma naman jakuna har 414.

Hukumar ta kama buhunan fatun da kuma naman jakin ne a watan Mayu inda ta damka su ga Hukumar Kula da Albarkatun Noma (NAQS).

Hukumar Kwastam ta kama buhunan naman jaki 414 a Kebbi
Hukumar Kwastan Lokacin Da Take Nuna Kayayyakin da Kwato. Hoto: Daily Star Nigeria.
Asali: Facebook

Hukumar ta kama babbar mota dauke da buhunan ne a kan hanyarsu ta zuwa Kambara da ke jihar Kebbi suna kokarin ficewa daga kasar, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Har Amnesty International Ta Fadi Adadin Mutanen da Aka Kashe a Gwamnatin Tinubu

Ben ya ce an kama buhunan naman jakin ne dalilin hadin kan jami'an tsaro

Shugaban hukumar reshen jihar, Dakta Ben Oramalugo yayin mika kayan ga NAQS a birnin Kebbi ya ce an samu nasara ne saboda hadin kan da suka samu daga sauran jami'an tsaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa kayan ana daf da fita da su wajen Najeriya ne lokacin da hukumar su ta yi nasarar kama wata babbar mota shake da kayan a iyakar jihar Kebbi.

Ben ya ce yayin wannan samame an kai wa jami'ansu farmaki tare da fasa musu motarsu amma hakan bai sa sun gajiya ba, sai da suka kwato kayan.

Ya gargadi masu aikata rirn wannan laifuka

Vanguard ta tattaro cewa Ben ya gargadi masu aikata irin haka da su sauya jiha domin zai mayar da jihar Kebbi gidan zuma ga masu aikata laifuka.

Kara karanta wannan

Kaduna: NAFDAC Ta Yi Dirar Mikiya A Kamfanin Hada Magungunan Gargajiya Na Babban Aisha, Ta Rufe Kamfanin

A karshe ya godewa jami'ansa da irin jajircewarsu da kokarinsu inda ya roke su da su ci gaba da zakulo bata gari da ke son kawo cikas ga zaman lafiya.

Kwastam Na Kokarin Hana Shigo Da Gwanjo Najeriya

A wani labarin, Hukumar Kwastam a Najeriya ta na kokarin hana shigo da kayan sawa na gwanjo kasar.

Kakakin Hukumar, Abdullahi Aliyu Maiwada ya bayyana cewa shigo da kayan nada illa ga kasa.

A cikin hirar da akayi da shi kakakin hukumar ya bayyana irin illolin shigo da kayan ke da shi ga 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel