Har Amnesty International Ta Fadi Adadin Mutanen da Aka Kashe a Gwamnatin Tinubu

Har Amnesty International Ta Fadi Adadin Mutanen da Aka Kashe a Gwamnatin Tinubu

  • Amnesty International ta na cigaba da bin lissafin duk wasu kashe-kashe da miyagu su ka yi a Najeriya
  • Kungiyar kare hakkin Bil Adamar ta ce alkalumanta sun nuna an kashe mutum 120 a zamanin Bola Tinubu
  • Shugaban Amnesty International ya ce dole ne gwamnatin Bola Tinubu ta dage wajen kare jinin al’umma

Abuja - Kungiyar nan ta Amnesty International mai ikirarin kare hakkin Bil Adama, ta yi magana a game da kashe-kashen da ake yi a Najeriya.

A wani bayani da aka samu a shafin kungiyar, an ji cewa sabon Darektanta na Najeriya, Isa Sanusi ya ce an zubar da jini a ‘yan kwanakin nan.

Mista Sanusi wanda shi ne shugaban rikon kwarya na Amnesty International, ya ce mutum akalla 123 su ka mutu daga 29 ga watan Mayu zuwa yau.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan PDP Ya Zama Babban Mai Yabon Gwamnatin Tinubu Dare da Rana

Tinubu
Bola Tinubu ya na kallon fareti: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne Bola Ahmed Tinubu ya karbi mulki a hannun Muhammadu Buhari, ya dare kan kujerar shugabancin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin shugaban Amnesty Int'l

“Abin tsoro ne cewa hare-haren ‘yan bindiga sun ci akalla mutane 123 makonni kadan da hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki a ranar 29 ga Mayu.
Kauyuka da kullum su ke zaune a shirin kawo hari, su na fuskantar munanan kashe-kashe. Dole gwamnatin nan ta maida hankali a kare rayuka.
Ya zama dole hukumomin Najeriya su dauki matakin gaggawa domin hana cigaba da zubar da jini.
Gazawar hukuma wajen kare mutanen Najeriya ya na neman zama ba-komai ba a kasar nan. Gwamnatin nan ta yi alkawarin ba jama’a kariya.
Sai dai har yanzu ba a cika alkawarin nan ba, ba a ga wani yunkurin kirki daga gwamnatin Najeriya wajen bada kariya ga al’umma masu rauni ba.

Kara karanta wannan

Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka

- Isa Sanusi

Ya kamata ayi bincike na musamman

Sanusi ya bukaci a binciki duka kashe-kashen da aka yi domin a hukunta masu wannan danyen aiki.

Kungiyar ta ce an rasa rayuwa fiye da 150 kauyukan Mangu, Katako da Kusherki a jihar Filato, sannan an kashe Bayin Allah sama da 100 a Benuwai.

A jihar Kaduna, mutane fiye da 100 ‘yan bindiga su ka hallaka daga Disamba zuwa Afrilu.

Tinubu ya cika alkawarinsa

A wani rahoto da mu ka fitar, an ji labari matakin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya dauka zai yi sanadiyyar arzikin matasa da-dama a kasar nan.

Mutum kusan rabin miliyan daya ake hasashen sabuwar dokar kare bayanai za ta nemawa aiki. Tinubu ya fara cika alkawuran da ya yi wajen kamfe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel