An Bukaci Kotu Ta Dakatar Da EFCC Daga Bincikar Ganduje Kan Bidiyoyin Dala

An Bukaci Kotu Ta Dakatar Da EFCC Daga Bincikar Ganduje Kan Bidiyoyin Dala

  • An bukaci babbar kotu a Kano da ta dakatar da hukumar EFCC daga binciken tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje
  • A 2018 ne dai wasu bidiyoyi suka bayyana inda aka zargi Ganduje da karbar daloli daga wajen wani mai aikin kwangila
  • Tsohon Atoni janar na jihar Kano ya shigar da wata kara kan EFCC cewa bata da hurumin binciken shari’ar da ke gaban majalisar jihar

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bukaci babbar kotun jihar da ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) daga gayyata ko bincikensa a kan bidiyon da ya nuno shi yana karbar daloli, jaridar The Cable ta rahoto.

Wani bidiyo dai ya yadu a soshiyal midiya a 2018 inda ake zargin Ganduje da karbar daloli yana zubawa a babban rigarsa daga wajen wani mai aikin kwangila.

Kara karanta wannan

Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje
An Bukaci Kotu Ta Dakatar Da EFCC Daga Bincikar Ganduje Kan Bidiyoyin Dala Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Yayin da gwamnan ya yi watsi da bidiyoyin, majalisar dokokin jihar Kano ta kafa wani kwamiti domin ya binciki zarge-zargen da ake yi wa gwamnan.

Har yanzu kwamitin bai gabatar da rahotonsa ba kuma har an rantsar da sabuwar majalisa a ranar Talata, 13 ga watan Yuni a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ki hana EFCC bincikar Ganduje, tsohon Atoni Janar na Kano ga Kotu

A wata kara da ya shigar, tsohon atoni janar na jihar Kano ya bukaci kotu da ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa daga bincikensa har sai an yanke hukunci kan wani shari'a tsakanin Ganduje da Jafaar Jafaar, mawallafin jaridar Daily Nigerian.

Hukumar EFCC kadai ake tuhuma a cikin karar.

Ganduje, ta hannun tsohon atoni janar na jihar Kano, ya bukaci kotu da ta ayyana gayyata da yi wa shugaban SUBEB da akanta janar na Kano tambayoyi dangane da bidiyon a matsayin wanda baya bisa ka'ida.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Da Ke Gab Da Yin Aure Ya Rasa Ransa Sakamakon Nutsewa A Ruwa A Enugu

Daily Trust ta lura cewa an shigar da karar gaban kotu tun a ranar 23 ga watan Maris, yan kwanaki bayan zaben gwamna wanda jam'iyyar adawa ta yi nasara.=

Sai dai kuma, an lura cewa takardun sun isa ga EFCC ne a ranar 5 ga watan Yuni.

Yayin da sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bai yi wata sanarwa dangane da bidiyon ba tun bayan da ya hau kujerar mulki, wata kungiyar jama'a mai yaki da rashin gaskiya ta bukaci EFCC da ta gurfanar Ganduje tun da a yanzu ba shi da kariya.

Ina tursasawa matata yi wa yan uwa na sanatoci alfarma - Sanata Bulkachuwa

A wani labari na daban, mun ji cewa Adamu Bulkachuwa, sanata mai wakiltan Bauchi ta arewa, ya yi wani gagarumin fallasa game da harkokin matarsa a matsayinta na mai shari'a.

Dan majalisar na Bauchi ya bayyana cewa Zainab Bulkachuwa, matarsa, ta yi amfani da mukaminta a matsayin mai shari'a wajen yi wa takwarorinsa a majalisar dattawa alfarma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel