Gata Ga Dalibai: Muhimman Abubuwa 9 da Kowa Ya Kamata Ya Sani Game da Rancen Dalibai Na Tinubu

Gata Ga Dalibai: Muhimman Abubuwa 9 da Kowa Ya Kamata Ya Sani Game da Rancen Dalibai Na Tinubu

  • Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a dokar da za ta ba wa dalibai rance don inganta rayuwarsu, kamar yadda ya yi alkawari a yakin neman zabe
  • Dokar za ta ba wa dalibai 'yan Najeriya damar karbar rancen kudin yin karatu karkashin bankin ba da rance na dalibai a kasar
  • Tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila shi ya kirkiri dokar kuma aka tabbatar da ita kafin rusa majalisa ta tara

Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu akan dokar da za ta ba wa dalibai rance kamar yadda ya yi alkawari a lokacin gangamin yakin neman zabe.

Daya daga cikin masu ba wa shugaban shawara a harkar yada labarai, Dele Alake shi ya bayyana hakan a ranar Litinin 12 ga watan Yuni a Abuja, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Fastoci Sun Waigo Ga Tinubu da Wasu Bukatu, Sun Ce Dole ya Cika Musu Alkawari

Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar ba wa dalibai rance
Shugaban Kasa, Bola Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Da Za Ta Ba Wa Dalibai Rance. Hoto: Channels TV.
Asali: Facebook

Dokar ba da rancen za ta kasance karkashin ma'aikatar ilimi

Alake ya ce kudin zai kasance karkashin ma'aikatar ilimi kuma daliban gaba da sakandare kadai ne da basu da hali za su samu damar amfana da kudin, cewar gidan talabijin na Channels.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abubuwan da ya kamata ku sani game da dokar rancen kudi ga dalibai

1. Tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila shi ya kirkiri dokar kuma aka tabbatar da ita a cikin makwanni biyu kafin rusa majalisa ta tara.

2. Dokar za ta kirkiri bankin ilimi na Najeriya da zai kula da yadda tsarin ba da rancen zai kasance ga dalibai.

3. Daliban za su nemi rancen ne ta makarantar gaba da sakandare da suke ciki a kasar.

4. Duk dalibin da yake sha'awar rancen za a tantance shi don tabbatar da ya cika ka'idoji.

Kara karanta wannan

Majalisa ta 10: Tajudden ya kara hango haske, babban abokin hamayyarsa ya janye daga takara

5. Sunan dokar ita ce "Dokar da za ta ba da rance ga daliban makarantar gaba da sakandare ba tare da kudin ruwa ba, don inganta ilimi a kasar".

6. Dokar ta na da karfin da za ta tsaya da kafafunta a kowa ne yanayi da kuma tsari.

7. Duk yadda wata doka ta fada, dalibai za su iya neman rancen kudaden don yin karatu a kasar.

8. Dokar ba ta da alaka da daliban da ke son karatu a kasashen ketare

9. Wannan dokar gwamnatin Najeriya ne da ke son taimakawa 'yan Najeriya da ke son inganta rayuwarsu ba tare da barin kasar ba.

Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Bai Wa Dalibai Bashi

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin da zai ba wa dalibai damar karbar rancen kudi don inganta karatunsu.

Dele Alake daya daga cikin masu ba wa shugaban shawara shi ya bayyana haka a fadar shugaban kasa a ranar Litinin 12 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel