Shugaba Buhari Ya Amince da Rabon Sababbin Mukamai a Hukumar FERMA

Shugaba Buhari Ya Amince da Rabon Sababbin Mukamai a Hukumar FERMA

  • Muhammadu Buhari ya sabunta wa’adin ‘yan majalisar da ke kula da aikin hukumar FERMA
  • Shugaban Kasa mai barin-gado ya nada James Akintola ya maye gurbin Tunde Lemo a Hukumar
  • Kafin a ba Akintola kujerar hukumar gyara titunan, ya yi aiki a jihohin Kwara, Oyo da Legas

Abuja - Shugaba Muhammau Buhari ya amince a canza shugabannin majalisar da ke kula da FERMA mai kula da gyaran titunan tarayya.

Premium Times ta ce Mai girma Muhammadu Buhari ya sabunta wa’adin sauran shugabannin da ke sa ido a aikin hukumar FERMA.

Sabon shugaban majalisar shi ne James Akintola wanda ya canji Tunde Lemo bayan ya amince ya sauka kan mukamin da yake rike da shi.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari wajen kaddamar da littafi Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Sauran shugabannin majalisar za su zarce a kan mukamansu zuwa lokacin da wa’adinsu zai cika.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wanene James Akintola

Kafin yanzu, Akintola wanda kwararren masanin zane ne ya rike irin wannan mukami a jihohi dabam-dabam a Kudu da Arewacin kasar.

Akintola ya yi Digirinsa na farko da na biyu a ilmin zayyana a Jami’ar Legas da kuma Jami’ar Obafemi Awolowo wanda aka sani da Ife a baya.

Rahoton ya ce a baya, Akintola ya taba zama babban mai bada shawara a kan harkokin gina abubuwan more rayuwa ga gwamnatin Oyo.

Sabon shugaban majalisar na FERMA ya yi aiki da gwamnatin jihar Kwara sannan ya rike shugabancin hukumar ayyukan jama’a a Legas.

The Cable ta ce jawabi ya fito daga Mai magana da yawun bakin shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya na tabbatar da nadin.

Aikin hukumar FERMA

Majalisar tarayya suka kafa hukumar FERMA a 2002, sannan ta fara aiki a shekarar 2023. Akwai Darektoci da ke kula da duka aikace-aikacen ta.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

Shi kuwa Tunde Lemo ya yi aiki a babban bankin kasa na CBN kafin rike wannan kujera.

An kai Tinubu kotu

An ji labari an shigar da sabuwar kara a kan Bola Tinubu a kotun Abuja a madadin kungiyar ASRADI a kan rantsar da sabon shugaban kasa.

Kungiyar nan ta ASRADI ta na so a hana Tinubu jin kanshin Aso Villa, ta ce zababben shugaban kasar ya yi wa INEC karya a wajen cike fam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel