Gobara Ta Tashi a Sansanin Rundunar Sojin Sama a Birnin Abuja

Gobara Ta Tashi a Sansanin Rundunar Sojin Sama a Birnin Abuja

  • Gobara ta tashi a wasu sassan sansanin hukumon sojin saman Najeriya har ta yi sanadin fashewar tankin man Fetur
  • Daraktan yaɗa labarai na NAF, Air Commodore Ayodele Famuyiwa, ya ce zuwa yanzu sun samu nasarar kashe wutar
  • Ya ce abun farin cikin da godiya babu wanda ya mutu sanadin wutar kuma sun fara bincike

Abuja - Wuta ta kama a wasu ɓangarorin sansanin hukumar sojin saman Najeriya da ke Titin filin jirgin sama a birnin tarayya Abuja.

Channels tv ta rahoto cewa har yanzun ba bu wanda ya san musabbabin tashin wutar yau Laraba 10 ga watan Mayu, 2023.

NAF Abuja.
Gobara Ta Tashi a Sansanin Rundunar Sojin Sama a Birnin Abuja Hoto: channelstv
Asali: UGC

Tuni jami'an hukumar kashe gobara suka fara kokarin shawo kan wutar kuma har yanzun rundunar sojin sama ba ta yi wani jawabi a hukumance ba.

Yayin da wakilin jaridar Punch ya tuntubi daraktan sashin ayyuka na hukumar kashe gobara reshen Abuja, Amiola Adebayo, ya ce jami'ansu na aiki ba ji ba gani don kashe wutar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Roki Majalisa Ta Bada Damar Ya Karbo Aron $800m a Karshen Mulkinsa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Adebayo ya ce:

"Gobara ta tashi a wasu sassan sansanin NAF, kuma jami'an mu sun dira wurin sun fara kokarin shawo kan wutar. Muna iya bakin kokarinmu domin kashe wutar baki ɗaya."
"A halin yanzu ba zan iya tabbatar da abinda ya haddasa tashin wutar ba, amma da zaran mun gama bincike zamu sanar da abinda muka gano a hukumance."

NAF ta tabbatar da faruwar lamarin

A wata sanarwa, daraktan yaɗa labarai na NAF, Air Commodore Ayodele Famuyiwa, ya ce rundunar sojin ta fara bincike kan abinda ya faru.

Ya nuna godiyarsa ga Allah saboda babu wanda wutar ta yi ajalinsa kana ya jinjina wa kokarin jami'an hukumar kiyaye haɗurra, Cibil Defens da sauran hukumomin tsaron da suka kawo ɗauki don kashe wutar.

Daraktan ya ce:

"Tuni jami'an kwana-kwana daga filin jirgi, hukumar kashe gobara ta tarayya da NAF suka haɗu suka kashe wutar, wacce ta haddasa fashewar tankin Fetur."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Bar Najeriya Zuwa Ƙasar Turai, An Bayyana Abu 2 da Zai Maida Hankali

"Mun gode wa Allah babu wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon gobarar. A yanzu mun fara binciken kwakwaf domin bankaɗo abinda ya jawo wutar ta kama."

Jami'an tsaro sun daƙile harin yan bindiga a PLASU

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Hostel Ɗin Ɗalibai Mata a Jami'ar Jihar Filato

Jami'ar jihar Filato ta tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun yi yunkurin sace ɗalibanta mata da daren ranar Talata zuwa wayewar garin Laraba.

A cewar kakakin jami'ar, dakarun tsaron makarantar sun yi nasarar dakile harin ba tare da maharan sun ɗauki ko mutum ɗaya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel