Kiwon Lafiya: Alfanun Shan Nonon Iyali 7 Ga Mace Da Kuma Namiji

Kiwon Lafiya: Alfanun Shan Nonon Iyali 7 Ga Mace Da Kuma Namiji

  • Masana lafiya sun tabbatar da cewa shan mama ga mace na da alfanu mai yawa
  • Haka su ma ga maza shan maman kan inganta lafiyarsu da kuma garkuwar jikinsu
  • Don haka masanan ke shawartar mata da su dinga bari mazajensu su sha ruwan mamansu

Masana kiwon lafiya dai sun shawarci maza da shan maman matansu a wani shiri da duniya ta ɓullo da shi domin wayar wa da kai game da illar cutar da daji na mama.

Wani ƙwararre a fannin lafiya kuma shugaban kamfanin Magunguna na Tsirrai ne ya yi wa wannan wata na Oktoba take da "Watan Shan Mama" domin ƙarfafa wa maza guiwa wajen shan mama.

Mama a cikin mace wata matattara ce da jijiyoyi masu kai saƙonni da suke motsuwa idan aka taɓa ko aka sha maman.

Maza da yawa na sha'awar shan mama kamar yadda su matan ke don a motsa su.

Sai dai wasu mazan kan gujewa shan maman matansu da zarar sun ɗauki juna biyu saboda a tunaninsu ruwan maman na da illa ga manya.

Ruwan mama dai ba kawai domin jirajirai ka yi shi ba, domin yana da alfanu ga manya. Yana ƙara wa manya ƙarfin garkuwar jikinsu kamar yadda yake yi wa yara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mother
Kiwon Lafiya: Alfanun Shan Nonon Iyali 7 Ga Mace Da Kuma Namiji

ALFANUN SHAN MAMA GA MATA:

1-YANA INGANTA LAFIYAR ZUCIYA

Shan mama na taimaka wa kafofin numfashi. Idan aka sha maman mace na tsawon lokaci, hakan na ƙara saurin bugawar zuciyarta sau 110 a mintuna ɗaya.

Wannan wani samfurin motsa jiki ne ga zuciya.

2-YANA INGANTA YANAYIN FUSKA DA WASHEWAR FATA.

Idan kina son washewar fuska, to lallai ke dage wajen mijinki ya sha mamanki. Sannan ki zama mai tuna masa idan ya manta.

Dalili kuwa shi ne, yana taimakawa wajen bunƙasar tsokar fuska da kuma inganta tafiyar jini a fatarmu wanda hakan ke sa fatar mu ta washe.

Haka kuma, idan ke marar samun sha'awar saduwa ce, ke ƙarfafa wa mijinki ya sha mamanki da kuma wasa da kansu, kafin ki ce kwabo za ki samu gamsuwa.

3- YANA ƘARA ƘARFIN GARKUWAR JIKI

Shan mama magani ne da ke ƙara wa garkuwa jiki ƙarfi da ke samar da ƙwayoyin yaƙi da ƙwayar cuta. A yayin da ake shan maman, numfashin mace kan ƙaru sau 60 a minti ɗaya.

Shaƙar iska da kuma fitar da ita a-kai-a-kai na magance cututtuka masu yawa da suka shafi hunhu.

4-RAGE YIWUWAR KAMUWA DA CUTAR DAJI.

Bincike ya tabbatar da cewa, shan mama da lallatsa yana rage yiwuwar kamuwa da matsalar kumburi wanda ka iya zama cutar daji.

Hakan na taimakawa wajen zirga-zirgar homon da kuma hana kumburi.

ALFANUN SHAN MAMA GA MAZA.

An tabbatar da cewa ruwan mama yana taimaka wa yara kamar yadda yakan taimaka wa manya ma.

Ga dai wasu daga cikin alfanun hakan ga maza:

1- RUWAN MAMA NA HANA KAMUWA DA CUTAR DA JI DA ƘARFAFA GARKUWAR JIKI DA NARKEWAR ABINCI

A matsayinki na mai sha'yarwa, idan mijinki yana yana son ya sha mamanki, ka da ki hana shi saboda yana taimaka masa wajen ƙara ƙarfin garkuwar jikinsa da kuma narkewar abinci.

Manya da ke da cutar daji, matsalar narkewar abinci ko raunin garkuwar jiki, akan shawarce su da su sha madara ko nono domin rage waɗannan matsaloli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel