Yadda Sojoji Suka Farmaki Ofishinmu Na Kebbi, Sun Yi Wa Ma’aikatanmu Mugun Duka – Kamfanin Wutan Kaduna

Yadda Sojoji Suka Farmaki Ofishinmu Na Kebbi, Sun Yi Wa Ma’aikatanmu Mugun Duka – Kamfanin Wutan Kaduna

  • Jami'an sojoji sun farmaki ma'aikatan kamfanin wutar lantarki na KAEDCO a jihar Kebbi
  • Sojojin sun yi wa ma'aikatan mugun duka kan zargin yanke masu wuta a sansaninsu na Dukku da ke Birnin Kebbi
  • Kamfanin wutar lantarkin na Kaduna ya sha alwashin daukar mataki na doka cewa lafiyan ma'aikatansu na da muhimmanci

Jami'an kamfanin wutar lantarki na Kaduna sun dandana kudarsu lokacin da sojoji suka farmaki kamfanin da ke jihar Kebbi inda suka yi wa ma'aikatan da ke bakin aiki dukan tsiya.

An tattaro cewa sojoji sun farmaki kamfanin ne a ranar Asabar kan zargin yanke wutar lantarki da ke sansanin sojoji na Dukku da ke Birnin Kebbi, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Sojoji a cikin mota
Yadda Sojoji Suka Farmaki Ofishinmu Na Kebbi, Sun Yi Wa Ma’aikatanmu Mugun Duka – Kamfanin Wutan Kaduna Hoto: Independent
Asali: Facebook

Da yake watsi da lamarin, shugaban sashin sadarwa na kamfanin lantarkin Kaduna, Abdulazeez Abdullahi, ya ce sojojin basu taba kai korafi dangane da aikinsu ba kafin suka farmaki ma'aikatansu.

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Cika Hannu Da Yan Sara-Suka 98 a Wata Jihar Arewa

"A zahirin gaskiya, yunkurin da tawagarmu a jihar Kebbi suka yi inda suka bukaci ganawa da rundunar sojin don tattauna batutuwa ya ci tura.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun yi watsi da cin zarafin ma'aikatanmu da rundunar sojojin Najeriya suka yi a Birnin Kebbi.
"Dakarun sojojin sun farmaki harabarmu a ranar Asabar sannan suka farmaki wasu ma'aikata da kwastamomi.
"Sojojin sun yi wa mutanen mugun duka tare da cin mutunci ba tare da dalili ba. Irin wannan ta'asar bai da gurbi a al'ummar da muke ciki.
"Muna burin fitowa fili mu ce kamfanin lantarkin Kaduna ba zai ba da tabbacin aikinsa ba saboda rashin tsaro. Lafiyar ma'aikatanmu na da matukar muhimmanci.
"Bama yarda da irin wannan tsoratarwa da cin zarafin ma'aikatanmu kuma za mu dauki matakin da ya dace da doka don neman gyara."

Majiya a sansanin soji ta yi martani

Kara karanta wannan

Binani ce ta ci zabe: Hudu Ari ya fasa kwai, ya ce manya a INEC sun karbi cin hanci daga Fintiri

Wata majiya a sansanin sojojin ta ce:

"Duba ga lamarin tsaron a kasar nan, musamman a yankin arewa, ya kamata KAEDCO ta yi taka-tsan-tsan wajen katse duk wata kafa na sojoji.
"Barin sansanin sojoji kamar sansanin Dukku, inda ake ajiye manyan makamai cikin duhu yana da matukar hatsari."

Yan sanda sun kama yan Sara-Suka 98 a Kaduna

A wani labarin, rundunar yan sanda a Kaduna sun kama wasu yan Sara-Suka 98 da suka addabi al'umma a garuruwan jihar.

Jami'an tsaron sun kwato muggan makamai da suka hada da wukake, almakashi, tabar wiwi da abubuwan da suke amfani da shi wajen farmakar mutanen da suka ci karo da su a hanya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel