Rundunar Yan Sanda Ta Kama Yan Sara-Suka 98 a Jihar Kaduna

Rundunar Yan Sanda Ta Kama Yan Sara-Suka 98 a Jihar Kaduna

  • Jami'an yan sanda a Kaduna sun yi nasarar kama yan Sara-Suka 98 a wasu samame da suka kai a jihar
  • Yan sara-suka sun addabi al'ummar jihar inda suke yi masu kwacen wayoyi, da sauran muhimman kayayyaki
  • Gwamna Nasir El-Rufai ya yi umurnin bibiyar sauran yan kungiyar da suka tsere tare da gurfanar da su

Kaduna - Rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta samu gagarumin nasara a kan yan Sara-Suka da suka addabi al'ummar jihar inda suka kama mambobin kungiyar 98.

Hakan ya biyo bayan umurnin da Gwamna Nasir El-Rufai ya bayar ne inda ya nemi dauki mummunan mataki kan yan miyagun da suka addabi al'umma, jaridar The Guardian ta rahoto.

Jami'an yan sanda
Rundunar Yan Sanda Ta Kama Yan Sara-Suka 98 a Jihar Kaduna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yan daban suna farmakar mutane inda suke kwace masu wayoyi da sauran kayayyakinsu, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da kuma raunata bayin Allah da basu ji ba basu gani ba a jihar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Aka Yi Wa Wasu Matasa Biyu Yankan Rago a Jihar Filato

A cewar rahotanni, an kama masu laifin 98 tsakanin ranar 26 ga watan Afrilu da 28 ga watan Afrilun 2023. Daga cikin adadin, an kai 19 kotu, yayin da har yanzu ake kan binciken sauran mutum 61 a ofishoshin yan sanda daban-daban a birnin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tura mutane 18 din da aka kama zuwa sashin binciken laifuka don ci gaba da bincike gabannin gurfanar da su.

Wata sanarwa daga kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya ce:

"Rahoton ya kuma bayyana cewa an kwato kayayyaki da dama daga wadanda ake zargin da suka hada da wayoyin sata, wukake, almakashi, tabar wiwi da magungunan maye iri-iri da kuma makullai da sauran muhimman abubuwa.
"Gwamnan ya bukaci rundunar da ta tabbatar da an hukunta su ba tare da tangarda ba, sannan ya yi umurnin a fara bibiyar wadanda suka tsere har sai an gurfanar da su gaban doka."

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kashe yaran da suka sace a Arewa, sun sako wasu 70

Kwamishinan ya kara da cewa:

"Gwamnan ya yi kira ga mazauna unguwanni kamar su Rigasa, Kawo, Ungwan Muazu, Badarawa, Kwaru, Rigachikun, Barnawa, Ungwan Rimi, Trikania, Nasarawa, Makera, Sabon Tasha, Narayi, Rafin Guza, Tudun Wada da sauran wurare, da su bayar da sunayen wadanda ake zargin yan kungiyar ne a yankunansu domin hukumomin tsaro su dauki mataki.
"Ana iya mika muhimman bayanai zuwa dakin tsaro ta hanyar lambobinsu 09034000060 da 08170189999.”

Yan sanda sun kama bindigogin AK-47 a jihar Kano

A wani labarin, rundunar yan sanda a jihar Kano sun kama wasu bindigogin AK-47 guda hudu a hanyar Kano zuwa Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel