“Har Yara 6 Sun Mutu”: NAFDAC Ta Yi Gargadi Game da Wani Magani Mai Kisa, Ta Tura Sakwanni Ta Imel

“Har Yara 6 Sun Mutu”: NAFDAC Ta Yi Gargadi Game da Wani Magani Mai Kisa, Ta Tura Sakwanni Ta Imel

  • Babbar Daraktar NAFDAC, Mojisola Adeyeye ta gargadi ‘yan Najeriya game da wani shahararren maganin tari na bogi da ke yawo;
  • A cewarta, NATURCOLD da ya kashe yara shida a Kamaru, kuma akwai yiwuwar ya iya shiga Najeriya a yi amfani dashi
  • An ce maganin ya sanya yaran samu nakasa a kodarsu lokacin da suka yi amfani da maganin, inji hukumomin lafiyan Kamaru

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta gargadi ‘yan Najeriya game da wani magani mai kisa da ke yawo a kasar, NATURCOLD.

Babbar Daraktar NAFDAC, Mojisola Adeyeye ce ta bayyana gargadin a ranar Laraba, 26 ga watan Afrilun 2023, kuma ta ce rahotanni sun ce maganin ya kashe yara shida a kasar Kamaru.

Daraktar ta NAFDAC ta ce, maganin na tari ne, kuma babu shi a jerin magungunan da ta amince dasu wadanda aka shigo dasu daga kasashen waje, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Taliyar karshe: Gwamnoni 36 za su gana da Buhari, za su roke shi abu 1 kafin ya sauka

NAFDAC ta gargadi masu shan maganin mura ba kan ka'ida ba
Hukumar kula da nagartar abinci da magani ta Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya kamata kowa ya kula, gargadin NAFDAC

Daga nan, ta ce ya kamata a kula da shigowa da kuma yawon magunguna marasa inganci, lasisi da tasiri a kasar nan, masu siya suke dubawa da kyau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kuma bukaci masu shigo da magunguna, dillalai da masu saye da su guji shigowa da amfani da bogin magani a kasar.

Ta yi karin haske da cewa, magungunan bogi suna shiga Najeriya ne ta kasashen makwabta, kuma ana siyar dasu ne a kasuwar bayan fage a Najeriya.

Ku sanar da NAFDAC motsin magungunan bogi

Ta yi kira ga dillalan da ke irin wadannan magungunan da su kai su ga ofishin NAFDAC mafi kusa domin daukar mataki.

Ta ce:

“Idan kunsan wani da ya yi amfani da irin wadannan kayayyakin ko kuma ya jikkata ta dalilinsa, ana shawartar irin wannan da ya nemi taimakon gaggawa na likita daga kowane asibitin kwararru.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

Rahotanni sun bayyana cewa, daraktar ta NAFDAC ta kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya da masu amfani da magani da su ke kai rahoton maganin da basu gamsu dashi ba zuwa ofishin NAFDAC mafi kusa dasu.

A cewar Adeyeye, ma’aikatar lafiya a kasar a jamhuriyar Kamaru ta gargadi jama’a da su nesanta kansu da amfani da maganin tari na NATURCOLD.

A gefe guda, NDLEA ta kama wani mutumin da ya shigo da kayan maye Najeriya daga kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel