Dalilin da Ya Sa Za Mu Gana da Shugaba Buhari, Gwamnoni Sun Yiwa ’Yan Kasa Bayani

Dalilin da Ya Sa Za Mu Gana da Shugaba Buhari, Gwamnoni Sun Yiwa ’Yan Kasa Bayani

  • Gwamnan jihar Sokoto ya bayyana cewa, gwamnoni 36 za su gana da Buhari don tattauna wasu batutuwa masu muhimmanci
  • Ya ce za su gana dashi ne kan batun da ya shafi tattalin arziki da kuma kawo hanyar samar da kudin shiga ga kasa
  • Ya shaida kadan daga abin da gwamnonin suka tattauna a kai a ganawar da suka yi ranar Laraba da ta gabata

FCT, Abuja - Gwamnonin Najeriya 36 za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa dashi game da samar da sabuwar hanyar samar da kudaden shiga tare da mika wa majalisa ta 9 kafin karewar gwamnatinsa.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar gwamnonin a jiya Laraba 26 ga Afrilu.

Kara karanta wannan

Jirgin saman NigeriaAir Zai Fara Tashi Kafin Shugaba Buhari Ya Bar Aso Rock – Minista

Buhari zai gana da gwamnoni
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kenan | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tambuwal ya ce, gwamnonin sun tattauna da Buhari game da lamuran da suka shafi kasa, dimokradiyya da shugabanci nagari, ciki har da batun da ya shafi CBN da kudaden haraji, PM News ta ruwaito.

Jawabin da gwamna Tambuwal ya yi

Da yake jawabi, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A yau, mun tattauna ka’idojin da Hukumar Leken Asirin Kudi ta Kasa (NFIU) ta fitar kan ka’idojin kudi da take aiki a kai wajen ganin an fitar da Najeriya daga jerin sunayen masu ba da harajin kudi.
“Mun kuma tattauna batun ayyana samar da kananan asibitoci da ci kuma gaban da aka samu ya zuwa yanzu. A yayin bitarmu, wasu jahohin da suka samu wasu nasarori za su sami wasu kyautuka saboda kwazon da suka yi.
“Mun tattauna kan sabon tsarin kudaden shigar da hukumar tattara kudaden shiga ta RMFC ta mika wa shugaban kasa da kuma bukatar mu tuntubi shugaban kasa kan bukatar ya gabatar da sabon daftarin tsarin ga majalisar kasa kafin wannan gwamnatin ta shude.

Kara karanta wannan

Mutum 7 da Buhari Ya Ba Mukami, Kafin a Je Ko Ina Ya Canza Shawara, Ya Sallame Su

“Mun kuma tattauna batun harajin shigo da kayayyaki da aka ajiye a babban bankin Najeriya.
“Muna aiki don ganin an fara biyan kudaden ga gwamnatin tarayya da kuma jihohi.”

Tinubu ya koma gidan gwamnati na Defence House

A wani labarin, kunji yadda Bola Ahmad Tinubu ya koma gidan da gwamnatin tarayya ya bashi gabanin rantsar dashi.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da jiran ranar da za a rantsar da Tinubu a watan Mayu.

Ya zuwa yanzu, zai zauna tare da Shettima a Defence House kafin daga bisani ya koma Villa don ci gaba da mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel