Shugaba Buhari Ya Aike Da Sakon Murnar Sallah Ga 'Yan Najeriya, Ya Bayyana Wata Babbar Nasara Da Ya Samu

Shugaba Buhari Ya Aike Da Sakon Murnar Sallah Ga 'Yan Najeriya, Ya Bayyana Wata Babbar Nasara Da Ya Samu

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aike da saƙon Sallah ƙarama na ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa
  • Shugaba Buhari ya yaba wa gwamnatinsa kan yadda ta gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan
  • Shugaban ƙasar ya ce ya bar kyakkyawan tarihin gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan wanda hakan ci gaba ne ga dimokuraɗiyya

Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi bajinta sosai a zaɓukan da aka gudanar a ƙasar nan, inda ya yi nuni da cewa an yi adalci a zaɓukan wanda ya sanya har wasu ƴaƴan jam'iyyar sa ta APC, suka sha kashi a zaɓen.

Shugaba Buhari ya ce ko sau ɗaya bai tsoma bakin sa ba kan zaɓe domin ba wani ko wata fifiko.

Shugaba Buhari ya taya ƴan Najeriya murnar Sallah
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari Hoto: @vanguard.com
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a cikin saƙon Sallah da ya aikewa ƴan Najeriya, ta hannun hadimin sa Garba Shehu.

Kara karanta wannan

Rikicin Sudan: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Ta Kasa Kwaso 'Yan Najeriya

Shugaba Buhari ya ce yadda aka yi zaɓen 2023 cikin kwanciyar hankali, zai shiga cikin tarihi a matsayin ɗaya daga manyan nasarorin da ya samu a gwamnatinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin saƙon Sallah da ya aikewa al'ummar Najeriya, shugaba Buhari ya yi bayanin cewa sakamakon zaɓukan sun yi daidai da alƙwarin da ya ɗauka na yin sahihin zaɓe.

A kalamansa:

"Ina alfahari cewa na samar da daidaito a tsakanin dukkanin ƴan takara ba tare da la'akari da jam'iyyun su ba domin yin adalci ga kowa."
"Sahihin zaɓe shine kaɗai abinda yake ƙara wa dimokuraɗiyya armashi, saboda murɗe abinda mutane suke so tauye dimokuraɗiyya ne."
"An yi gaskiya a zaɓukan wanda har wasu daga cikin ƴaƴan jam'iyya ta suka rasa kujerun su. Ban taɓa tsoma baki ba domin ba wani ɓangare fifiko a zaɓen."

Ya taya musulmai murnar kammala Ramadan

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Dau Zafi, Ya Yi Wa Shugaba Buhari Kakkausan Martani

A dangane da azumin watan Ramadan, shugaba Buhari ya taya musulmai murnar kammala azumin wannan shekarar cikin nasara.

Shugaban ƙasar yayi addu'ar Allah ubangiji ya amsa dukkanin ibadun su sannan ya ba su ladan ayyukan alkhairin da suka gudanar a watan. Ya kuma tunasar da cewa kada su manta da darussan da suka koya a lokacin watan azumin.

A cewarsa:

"Bai kamata mu manta da muhimman darussan azumi ba wanda suka haɗa da ƙara ƙarfafa dangantakar mu da marasa ƙarfi da talakawa a cikin al'umma."
"Bari daga cin abinci da abin sha a lokacin azumi ya sanya mun fahimci irin halin da waɗanda suke kwana ba su ci abinci ba suke ciki kowace rana."

Gwamnan Jihar Benue Ya Dau Zafi, Ya Yi Wa Shugaba Buhari Kakkausan Martani

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya yi wa shugaba Buhari martani mai kaushi.

Ortom ya caccaki shugaba Buhari inda ya ce ya kasa kare rayukan al'ummar ƙasar nan, musamman na jihar sa ta Benue.

Asali: Legit.ng

Online view pixel