Lafiya uwar jiki: Karanta sirruka 6 dangane da shan ruwan kwakwa
- da dama ba su da masaniyar akan dimbin amfani da albarkar da ke tattare da shan ruwan kwakwa, shan ruwan kwakwa nada matukar amfani mai yawa ga lafiyar jikin dan adam:
- Legit.ng ta samo Kadan Daga Cikin Amfanin Shan Ruwan Kwakwa Sune;
1. Idan ana shan ruwan kwakwa a-kai-a-kai, yana karawa gangar jikin dan’adam kuzari, sannan ya kori cutuka masu yawan gaske; cutar dake hana fitsari, basir, sanyi, ciwon mara da cutuka masu yaduwa.
2. Ruwan kwakwa ba kuzari kawai yake karawa ba, yana kara karsashi da ni’ima a zamantakewar aure. Sannan yana rigakafin kamuwa da cutar koda sakamakon kwarara da yake yi a gangar jiki.
3. Yana wanke mafitsara, sannan ya goge dukkan wani datti da yake marar dan’adam. Ruwan kwakwa yana taimakawa wajen narka abinci, kasancewar yana dauke da sinadari.
4. Idan ana shan sa a-kai-a-kai, yana hana kanana kwayoyin cutuka shiga jikin bil’adama. Wani karin tagomashi da yake da shi, za ka iya shan ruwan kwakwa mai yawan gaske, tun da ba ya dauke da sinadari mai kara kiba. Sai ma taimakawa da yake yi wajen rage kiba.
KU KARANTA: Abun da zanyi a 2019 - Fayose
5. Idan fatar mutum na kodewa, abin da yake da bukatar yi shi ne kawai, a samu auduga a riga dangwala ruwan kwakwa ana shafawa. Zai goge fatar tas, ta rika haske da sheki, kurajen da suke fitowa duk za su baje. Har ila yau, za a iya hada ruwan kwakwa da ruwa kawai, shi ma yana taimakawa kwarai.
6. Kamar yadda binciken masana lafiya ya tabbatar, ruwan kwakwa yana magance matsaloli masu yawa lokacin haihuwa. Shan ruwan kwakwa kofi guda a duk safiya yana daidaita zaman da a cikin mahaifiya, wanda karkacewar yaro a wasu lokutan yana haifar da ciwon hawan jini.
Har ila yau masana sun ce, idan mutum ya sha giya, ka’ida ne da safe kansa ya yi ciwo, saboda haka idan ya sha ruwan kwakwa, kan zai daina ciwo kuma marisar da yake yi za ta kau nan take.
A duk lokacin da aka yi wani babban aiki, wanda ya gajiyar da kai, za ka iya amfani da ruwan kwakwa domin warware gajiya nan take. A wannan mataki, ruwan kwakwa zai kara kuzari da karsashi, na yadda komai irin aikin da aka yi, za iya komawa a ci gaba.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng