Kungiyar NECA Ta Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Kan Karin Albashin Ma'aikata

Kungiyar NECA Ta Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Kan Karin Albashin Ma'aikata

  • Kungiyar NECA ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan yin gaggawa wurin yanke hukuncin dangane da karin albashin ma'aikata
  • Kungiyar ta ce jinkirin yana cigaba da haifar da matsalolin a tsakanin masu ruwa da tsaki a kan lamarin karin albashin da gwamnati
  • Ta kuma bayyana irin abubuwan da ya kamata a maida hankali game da su kafin yanke hukuncin a kan mafi ƙarancin albashin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kungiyar masana harkokin ma'aikatan Najeriya (NECA) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya kan yin gaggawa wurin kammala shirye-shiryen karin albashi.

shugaba Tinubu
NECA ta ce jinkirin karin albashi na jefa kokonto ga ma'aikata. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Matsalar jinkirin karin albashin ma'aikata

Kungiyar ta ce jinkirin zai kara haifar da kokonto da rashin yarda tsakanin ma'aikata da gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dawo da lantarki a garuruwan da aka yi shekaru babu wuta a Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa shugaban kungiyar ne, Adewale Smart Oyerinde ya bayyana haka ga manema labarai.

Mista Oyerinde ya kara da cewa jinkirin da gwamnatin ke yi ya kawo rashin fahimta tsakanin kungiyar kwadago da gwamnonin jihohi.

Ya kuma bayyana cewa zaman da kwamitin karin albashin ya yi na karshe ya kai sama da wata daya amma har yanzu ba a ji wani bayani ba.

Kiran shugaban NECA ga kungiyar kwadago

Shugaban kungiyar ya koka kan sabanin da aka samu tsakanin kungiyar kwadago da gwamnonin jihohi kan biyan N615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Sai dai ya yi kira ga dukkan bangarorin da su kai zuciya nesa da kuma jira kwamitin karin albashi na kasa ya fitar da nasa sakamakon, cewar jaridar the Sun

Duk da haka, ya kara da cewa dole ne karin albashin ya lura da irin nauyin da ke kan ma'aikata da kuma halin da ake ciki na tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Kungiya ta maka gwamnoni 36 da minista Wike a kotu kan cin bashin N5.9tn da $4.6bn

Tinubu ya amice da karin albashi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta sanar da yi wa ma'aikatan Najeriya ƙarin kudi a albashi.

A cewar sakataren yaɗa labarai na hukumar kula da albashi ta ƙasa ma'aikatan da ke kan tsarin albashi na bai ɗaya za su samu ƙarin albashi da kaso 25% zuwa kaso 30% a kan abin da suke karɓa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel