Gwamnati Ta Tsaida Ranar Kammala Manya-Manyan Ayyukan da Buhari Ya Tattago

Gwamnati Ta Tsaida Ranar Kammala Manya-Manyan Ayyukan da Buhari Ya Tattago

  • Ministan ayyuka da gidaje ya ce daga zuwa karshen Afrilu za a karkare aikin titin Legas-Ibadan
  • Amma Babatunde Fashola SAN ya ce ‘yan kwangila ba za su iya karasa hanyar Abuja-Kano ba
  • Ministan ya ce Gwamnatin tarayya ba ta soma aikin hanyar birnin Abuja-Kaduna-Kano da wuri ba

Abuja - Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Babatunde Raji Fashola ya ce za a gama babban titin Legas zuwa Ibadan zuwa ranar 30 ga watan Afrilun 2023.

Amma Premium Times ta rahoto Babatunde Raji Fashola yana mai cewa ba za a iya karasa aikin hanyar Abuja zuwa Kano cikin wa’adin gwamnatin nan ba.

Mai girma Ministan ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba yayin da ya je duba aikin gadar Loko-Oweto da ke jihar Nasarawa domin ganin halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

Ministan ya ba matafiya hakuri a kan aikin da ake yi a titin na Legas zuwa Ibadan, yake cewa aiki a hanyar yana da wahala saboda yawon motoci a kullum.

Titin Legas-Ibadan, saura kiris

Babatunde Fashola wanda ya ce motoci 40, 000 suke bin titin a rana, yake cewa ba za a iya toshe hanyar gaba daya domin kwangilar ba, sai dai a rika lallabawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Gwamnan ya yaba da kokarin jama’a, ya ce 30 ga watan Afrilu ne wa’adin kammala titin, ya ce a tsakiyar Mayu za a gama aikin gadar nan ta Neja.

Titin
Titin Loko-Oweto Hoto: @FMWHNIG
Asali: Twitter

A cewarsa, nan makonni hudu – kwanaki 26, ‘yan kwangila za su gama aikin kusan duka titin na Legas zuwa Ibadan, abin da zai rage bai fi kilomita tara ba.

Rahoton NAN ya ce abin da ya sa za a samu gibin shi ne gwamnatin jihar Oyo ta na gina hanyoyin ruwa kan titin, ana sa hakan zai yi maganin yawan ambaliya.

Kara karanta wannan

Easter: Buhari ya ba da hutun kwana 2 a Najeriya, ya roki 'yan Najeriya wata alfarma

Titin Abuja zuwa Kano

A game da hanyar Abuja zuwa Kano kuwa, Ministan ya ce kwangilarsa ta fi ta kowace titi girma a kasar nan, sannan shi ne ya fi kowane ci wa gwamnati kudi.

Titin mai tsawon kilomita 375 daga birnin tarayya Abuja zai tike a garin Kano, wanda yake dauke da gadoji ba zai kammalu zuwa karshen watan Afrilu ba.

Tribune ta ce Fashola ya bada uzurin abin da zai hana a kammala, ya ce aikin ne karshen farawa.

Amma duk da haka, aikin ya yi nisa musamman daga bangaren Zaria zuwa Kano, ‘yan kwangila za su gama a Mayu, kafin nan za a karasa Zariya-Kaduna.

Mukamai a gwamnati mai-zuwa

Rahoto ya zo cewa jama’a sun koma tunanin wadanda Bola Tinubu zai ba mukami a Gwamnatinsa idan ya dare mulki, yau saura kwanaki 53 a canza shugaba.

Ana hangen irinsu Femi Gbajabiamila da Nasir El-Rufai a gwamnatin zababben shugaban na Najeriya. Akwai yiwuwar a zakulo wadanda ba ‘yan APC ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel