Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Easter Guda Biyu Ga Ma’aikata a Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Easter Guda Biyu Ga Ma’aikata a Najeriya

  • Gwamnatin Buhari ta ba da hutun bukukuwan Easter a wannan watan, minista ya fitar da sanarwa mai daukar hankali
  • A cewar ministan, za a yi hutun a ranakun Juma’a da Litinin na wannan watan na Afrilu da ake ciki
  • Ministan ya yi kira ga kiristocin Najeriya da su sanya kasar a addu’ar fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali a irin wannan yanayin

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 7 da Litinin 10 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun Good Friday da Easter Monday.

Wannan na fitowa ne daga bakin ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Ogbeni Rauf Aregbesola a ranar Laraba 5 Afirilu, 2023 a Abuja.

Ministan ya yi kira ga Kiristoci a kasar da su yi riko da akidar sadaukarwa, hadin kai, yafiya, kirki, soyayya da hakuri a lokacin bukukuwan na Easter.

Kara karanta wannan

Rayyuka 17 Sun Salwanta A Sabon Rikici Da Ya Barke A Jihar Arewa

An ba da hutun kwanaki 2 a Najeriya a bukukuwan Easter
Rauf, ministan harkokin cikin gida a Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewarsa, halayen da ya bayyana a sama sun yi daidai da dabi’un Yesu Almasihu mai tsarki, kamar yadda rahoton The Nation ya bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran minista ga kiristocin Najeriya

A sanarwar da ministan ya fitar ta hannun sakataren dindindin na ma’aikatar, Dr Shuaib Belgore ya yi kira ga Kiristoci da su yi amfani da lokacin bukukuwan Easter wajen yiwa Najeriya addu’ar kawo karshen rashin tsaro.

Ya kara da cewa, lamarin da ya shafi tsaro aiki ne da a shafi dukkan ‘yan kasa na gari, inda ya kara da cewa, ya kamata ‘yan Najeriya da ma baki su saka kasar addu’a, rahoton Punch.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Najeriya na yin iyakar kokarinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin tsanaki ba tare da samun wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fadi Munanan Barazanar da Ake Fuskanta a Yau a Najeriya

Sarkin Musulmi ya yi kira ga a yiwa Najeriya a addu’a a Ramadana

A wani labarin, kunji yadda sarkin Musulmi a Najeriya ya bayyana ganin watan Ramadana, inda ya bukaci Musulmai da su dukufa da yiwa kasar addu’a a cikin watan.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da tashe-tashen hankula a bangarori daban-daban.

Ya kuma bayyana cewa, aikin tabbatar da tsaro a Najeriya na kowa ne, don haka akwai bukatar kowa ya dukufa a wannan fannin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel