Zamfara da Lagos ke Kan Gaba Wajen Samar da Kuɗin Shiga Na Cikin Gida

Zamfara da Lagos ke Kan Gaba Wajen Samar da Kuɗin Shiga Na Cikin Gida

  • A wani salon ban mamaki Zamfara ta haɗu da Legas a matsayin jihohi mafi samar da kuɗin shiga na cikin gida a shekaru 6
  • Kuɗaɗen kuɗin shigar an lissafta ne daidai da yadda darajar kudin ya ƙaru a cikin jihohin da ake magana akai
  • Kuɗin shiga na jihohi da yawa ya nuna ƙaruwa akan kuɗin da jihohi ke samarwa dake nuna rage dogaro ga gwamnatin tarayya

Wani bayani daya fita daga hukumar ƙididdiga ta ƙasa, ya nuna yadda jihohin Najeriya 36 ke samarwa kansu kuɗaɗen shiga na cikin gida.

Rahoton ya nuna yadda kuɗin shigar jihohi ya tashi daga biliyan N682.67 zuwa tiriliyan N1.76 a shekaru 6 da suka gabata watau daga (2015 zuwa 2021).

Duba na tsanaki ya nuna yadda yadda alƙaluman suka bambanta tsakanin jihohin.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Buhari, Sabon Gwamna Ya Bayyana Sabuwar Hanyar Yaƙi da 'Yan Bindiga

Gwamnoni
Zamfara da Lagos ke Kan Gaba Wajen Samar da Kuɗin Shiga Na Cikin Gida Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kuɗin shiga na cikin gida dai, shine kuɗaɗe da jihohi ke samarwa kansu domin gudanar da ayyukan cigaban raya ƙasa ba tare da an haɗa su da kuɗin da suke amsa daga gwamnatin tarayya ba.

Kuɗin shiga na cikin gida na da matukar muhimmanci saboda dashi ake amfani wajen yin alƙalancin yadda gwamna ya jagoranci jihar sa tare da ganin yadda kowacce jiha ta dogara da kanta.

Bugu da ƙari, jihohi dake da kuɗaɗen shiga na cikin gida mai yawa, ana kallon su da tattalin arziki mai kyau, wanda hakan ke janyo masu saka hannun jari.

Jihohi na samun kuɗaɗen shigar su na cikin gida ne yawanci daga, kuɗaɗen rasiti da ake biya, haraji, jangali, tare da sauran su.

Adadin Kuɗaɗen da Jihohi Suka Samu

Kara karanta wannan

Yadda Wani Tsoho Yayi Awon Gaba da Wayoyin Mutane 70

Daga 2015 zuwa 2021, jumullar abinda jihohi 36 suka samu ya fara daga 158.37 cikin ɗari ko kuma tiriliyan 1.8 Naira.

Binciken da jaridar Legit.ng ta gabatar ya nuna cewa, a cikin jihohi 36, guda 18 ne suka samu nasarar wuce adadi mafi kanƙanta na ƙasa akan batun kuɗaɗen shiga na cikin gida.

Jihohin da Suka fi Samun Haɓakar Kuɗaɗen shiga na cikin gida

  • Zamfara (592.39%)
  • Borno (431.41%)
  • Borno: (431.23%)
  • Nasarawa (382.07%)
  • Kaduna (358.31%)
  • Ekiti (313.60%)
  • Sokoto (281.09%)
  • Yobe (275.16%)
  • Kwara (276.20%)
  • Kogi (245.94%)
  • Plateau (209.45%)
  • Jigawa (224.13%)
  • Oyo (232.22%)
  • Bauchi (232.25%)
  • Kano (196.58%)
  • Ogun (191.38)
  • Kebbi (174.91%)
  • Niger (171.26%)

Idan kuma magana ake ta jihohi masu kuɗin shiga ta yawan ƙaruwar kuɗaɗen shiga ta kima, jihar Legas ita ce a gaba saboda ƙarfin tattalin arzikin ta, idan aka haɗa da sauran jihohi.

Kara karanta wannan

"Ban Taba Gani Ba", Bidiyon Wani Malamin Addinin Musulunci Na Huduba Cikin Harshen Igbo Ya Dauki Hankula

Alƙaluman sun nuna cewa, daga 2015 zuwa 2021, jihar Legas ta samu ƙari daga biliyan N268.22 zuwa biliyan N753.46 na bambanci haɓakar kuɗaɗen shiga ta kima.

Ga Jerin Sauran Manyan Jihohin Da Ke da Mafi Girman Ƙimar ci Gaban Kuɗaɗen shiga na Cikin Gida Samfurin Ƙima

  • Lagos - biliyan N485.23
  • Rivers - biliyan N123.35
  • Delta - biliyan N80.20
  • Ogun - biliyan N66.1
  • Kaduna - biliyan N52.86
  • Oyo - biliyan N52.09
  • Kano - biliyan N40.40
  • Akwa Ibom - biliyan N31.40
  • Edo - biliyan N23.30
  • Cross River - biliyan N22.91

China na Bin Duk Ɗan Najeriya N8,430 Yayin da Bashin Najeriya ya ƙara Haɓaka Zuwa $41bn

Ofishin kula da lamuni na ƙasa DMO, ya saki wani sabon rahoto dake nuna yadda bashin Najeriya yakai biliyan $41.

Alƙaluman na DMO ya nuna yadda bashin Najeriya yayi sama zuwa biliyan $4.46 tsakanin ta da China.

China nabin Najeriya bashi fiye da yadda Faransa da Jamus ke binta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel