Dan Takarar NNPP A Katsina Na So A Sake Kirga Kuri'un Zabe

Dan Takarar NNPP A Katsina Na So A Sake Kirga Kuri'un Zabe

  • Bayan rashin gamsuwa da sakamakon zaben majalisar mazabar Kurfi da ke Katsina, dan takarar NNPP ya tura korafi ga hukumar zabe
  • Dan takarar na bukatar hukumar INEC da ta sake kirga takardun kuri'a da aka yi amfani da su a zaben ranar 18 ga watan Maris a wasu mazabu da ke Kurfi
  • Hukumar zabe ta ce zata duba korafin tare da mayar da martani ga mai korafin kamar yadda ya dace

Katsina - Alhaji Shuaibu Iliyasu, dan takarar jam'iyyar NNPP na kujerar majalisar mazabar Kurfi a Jihar Katsina, ya nemi a sake kirga takardun kuri'a da aka yi amfani da su ranar 18 ga watan Maris a yankin.

Hakan na cikin wata takarda dauke da sa hannun lauyan sa, Muhammad Bello Gachi, da aka mika wa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC a Katsina, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yes Daddy', Dan Majalisar Kano Ya Kwaikwayi Peter Obi Bayan Ganawa Da Kwankwaso

Jami'ar NNPP
Dan Takarar NNPP A Katsina Na So A Sake Kirga Kuri'un Zabe. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An raba irin takardar, dauke da kwanan wata 23 ga watan Maris, 2023, ga manema labarai ranar Asabar a Katsina.

Takardar na dauke da taken, 'Bukatar sake kirga takardar kuri'a da aka gudanar da zabe, da ya gudana 18 ga watan Maris, 2023, a zaben majalisar jiha na Kurfi, Jihar Katsina'.

Kamar yadda takardar ta bayyana:

"Mu lauyoyi/wakikan kotun koli, mu ke magana a madadin Shu'aibu Iliyasu (wanda mu ke karewa) dan takarar NNPP a zaben majalisar jiha na Kurfi.
"Wanda mu ke karewa, bisa rashin amincewa da sakamako da aka sanar, wanda jami'an tattara zabe na Wurma(A), Wurma(B) da mazabun Barkiya, ya na kira ga hukumar, bisa ikon da ta ke da shi a sashe na 65 (1) na kudin zabe, 2022, ta sake duba sanar da sakamakon da jami'an tattara zaben suka yi.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Cafke Wani Ɓarawo Da Aka Daɗe Ana Nema A Jihar Arewa, An Ƙwato Motocci Daga Hannunsa

"Ta hanyar sake kirga duk takardun kada kuri'a a mazabun saboda an sanar da sakamako ba da niyya ba/ ko kuma an sabawa doka, ka'ida da kuma matakan sanarwa, da kuma hanyar gudanar da zabe.
"Yallabai, muna kira da a gaggauta gudanar da haka kafin hukumar ta sanar da lokacin gudanar da sake zabukan da ba su kammala ba a akwatunan da muka ambata a Kurfi da kewaye."

Bello-Gachi ya tabbatar cewa sun aikewa INEC takardar.

Lauyan hukumar zabe na Katsina, Naziru Salisu, shi ma ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa sun karbi takardar, ya ce zuwa Litinin, za su duba koken, tare da mayar da martani ga mai korafi kamar yadda ya dace.

Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin mika mulki ga zababben gwamna Abba Gida-Gida

A wani rahoto, Dakta Abdullahi Ganduje, gwamnan Kano mai barin gado ya kafa kwamiti na mutane 17 don mika mulki ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf, zababben gwamna.

Kara karanta wannan

Sayen kuri'u: An kori wata karar da ministan Buhari ya shigar kan Tinubu da Atiku

Asali: Legit.ng

Online view pixel