'Yes Daddy', Dan Majalisar Kano Ya Kwaikwayi Peter Obi Bayan Ganawa Da Kwankwaso

'Yes Daddy', Dan Majalisar Kano Ya Kwaikwayi Peter Obi Bayan Ganawa Da Kwankwaso

  • Ana cigaba da tattauna kan hirar wayar tarho da ta fito a kafafen watsa labarai da aka ce an yi tsakanin Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour da Bishop David Oyedepo na Winners Chapel
  • Kamar yada hirar ta bayyana, Obi ya kira babban malamin addinin yana neman ya taimaka ya umurci kiristocin wasu jihohin Kuda maso Yamma da Arewa maso Tsakiya su zabe shi, ya kira zaben a matsayin 'Yakin Addini'
  • A hirar an kuma ji yadda muryar da aka ce ta Obi ne na ta maimaita 'Yes Daddy' ma'ana 'Haka ne Baba' sau da dama a yayin da faston ke magana, zababben dan takarar majalisa a Kano, Sagir Koki shima ya ce 'Yes Daddy' bayan gabatar da satifiket dinsa ga Sanata Kwankwaso

Sagir Koki, zababben dan majalisar wakilai mai wakiltar Kano Municipal, ya kwaikwayi hirar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter, tare da Bishop David Oyedepo, mammallakin Living Faith Church Worldwide, da aka fi sani da Winners Chapel, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hirar Waya Da Aka Bankado: Babban Faston Najeriya Bishop Oyedepo Magantu Kan Tattaunawarsa Da Obi

Wata kafar watsa labarai na intanet, Peoples Gazette, a daren ranar Asabar ta saki murya inda aka ji Obi na bayyana zaben 2023 a matsayin yakin addini, abin na ta yaduwa a dandalin sada zumunta.

Kwankwaso
'Yes Daddy', Dan Majalisar Kano Ya Kwaikwayi Obi Bayan Ganawa Da Kwankwaso. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A muryar, an ji Obi yana rokon Oyedepo ya taya shi tattaro kuri'an kiristoci gabanin zaben, musamman a jihohin Arewa maso Tsakiya na Kwara, Kogi da Niger, yana bayyana abin a matsayin yakin addini.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ta nanata 'Yes Daddy', yayin hirar da suka yi a wayar.

An ji yana cewa a cikin muryar:

"Daddy, ina son ka yi wa mutanen ku magana a Kudu maso Yamma da Kwara, Kiristocin da ke Kudu maso Yamma da Kwara. Wannan yakin addini ne. Kamar yadda na saba fada; idan wannan ya yi aiki, ba za ku yi nadamar goyon baya na ba."

Kara karanta wannan

Inconclusive: Dan Takarar NNPP A Katsina Na So A Sake Kirga Kuri'un Zabe

Yayin da ya ke tabbatar da sahihancin muryar a daren ranar Lahadi, Kenneth Okonkwo, kakakin kwamitin kamfen din shugaban kasa na LP, ya yi ikirarin ba a fahimci hiran bane.

Da ya ke kwaikwayon Obi bayan gabatar da satifiket dinsa ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Koki ya rubuta:

"Thank You Daddy, Yess Daddy ❤️"

#YesDaddy yana da yaduwa a dandanlin sada zumunta.

Bishop Oyedepo Ya Yi Karin Haske Kan Tataunarsa A Wayar Tarho Da Obi

Shugaban Cocin Living Faith, Bishop David Oyedepo ya ce babu wani da ke fada masa abin da zai yi a rayuwarsa yayin martani kan hirar wayar tarho da aka bankado tsakaninsa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP.

A hirar, an jiyo Obi yana rokon Oyedepo ya taimaka ya roki kiristocin wasu jihohin Kudu maso Yamma da Kwara su zabe shi, inda ya kira zaben 'Yakin Addini."

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: Jerin jiga-jigan siyasan APC 3 da ke son maye gurbin Yahaya Bello da tasirinsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel