Ganduje Ya Kafa Kwamitin Mutum 17 A Kano Don Mika Mulki Ga Abba Gida-Gida, Cikakken Jerin Mambobi

Ganduje Ya Kafa Kwamitin Mutum 17 A Kano Don Mika Mulki Ga Abba Gida-Gida, Cikakken Jerin Mambobi

Jihar Kano - Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kafa babban kwamiti mai mutum 17 don mika mulki ga gwamnati mai jiran gado a jihar.

Majalisar ta kuma amince kafa wata karamar kwamitin mutum 100 da mambobinta za su fito daga ma'aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban, rahoton Daily Trust.

Ganduje
Ganduje Ya Kafa Kwamitin Mutum 17 Don Mika Mulki Ga Abba Gida-Gida. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Malam Muhammad Garba, kwamishinan labarai da harkokin cikin gida na jihar, ya ne fada wa manema labarai hakan bayan taron majalisar na mako-mako da aka yi a gidan gwamnatin Kano, yana mai cewa ana sa ran zababben gwamnan ya turo wakilai uku a babban kwamitin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce sakataren gwamnatin tarayya, Alhaji Usman Alhaji ne zai jagoranci kwamitin, daga cikin mambobi akwai shugaban ma'aikatan gwamnatin jiha, Antoni Janar/Kwamishinan Shari'a, Kwamishinan Labarai, Kwamishinan Muhalli, Kwamishinan Kasuwanci, Masana'antu Da Kungiyoyi.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnoni 36 Za Su Gana Da EFCC, CBN Don Yanke Shawara Kan Kudin Tsaro

Aikin Babban Kwamitin

Malam Garba ya ce babban kwamitin, za ta aiki cikin jituwa da nufin rubuta da shirya rahoton karshe na mika mulki a cikin makonni uku.

Kwamishinan ya ce an umurci babban kwamitin ta fara aikin shirye-shiryen mika mulki sannan ta lissafa nasarorin da aka samu a zango biyu na gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje.

Ya ce kwamitin kuma za ta yi nazarin rahoto daga hukumomi kan nasarorinsu ciki har da ayyukan da ake kan yi da suka shafi aiwatarwa, inda aka tsaya, matsaloli, kallubale daga ranar 25 ga watan Mayu zuwa yanzu.

Malam Garba ya ce babban kwamitin za ta kula da aikin karamar kwamitin wurin tattara bayanai da rahotanni tare da rubuta rahoton mika mulkin ga gwamnati mai jiran gado cikin sati hudu.

Ya ce Gwamna Ganduje zai kaddamar da kwamitin a ranar Talata misalin karfe 2 na rana a Africa House, Gidan Gwamnatin Kano.

Mambobin Kwamitin Mika Mulki a Jihar Kano

Kara karanta wannan

Abba Kabir Yusuf Ya Kafa Kwamitin Mutum 65 da Zai Karbi Mulki a Hannun Ganduje

1. Sakataren Gwamnatin Kano - Ciyaman

2. Shugaban Ma'aikatan Jiha

3. Antoni Janar/Kwamishinan Shari'a

4. Kwamishinan Labarai

5. Kwamishinan Muhalli

6. Kwamishinan Kasuwanci, Masana'antu Da Kungiyoyi

7. Kwamishinan Ayyuka Da Gine-Gine

8. Kwamishinan Kudi

9. Kwamishinan Ilimi

10. Kwamishinan Kasafin Kudi Da Tsare-Tsare

11. Kwamishinan Kananan Hukumomi

12. Direkta Janar na Hukumar Kula da Filaye na Kano

13. Direkat Janar Na Bincike Da Addana Bayanai

14. Shuagban Hukumar Tsara Birane Da Cigaba Na Kano

15. Wakilai uku daga zababben gwamna

Shugabanin kasasashen Cuba, Nicaragua da D8 sun taya Tinubu murna

A wani rahoton, kasashen duniya na cigaba da taya zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu murnar cin zaben.

Na baya-bayan nan suna shugaban kasashen Cuba da Nicaragua da kuma kungiyar kasashe masu tasowa ta D8.

Asali: Legit.ng

Online view pixel