"Na Fice Daga APC Domin Ta Gama Ɓata Mun Rai" - Mutumin da Yayi Wanka a Kwata Don Murnar Nasarar Buhari

"Na Fice Daga APC Domin Ta Gama Ɓata Mun Rai" - Mutumin da Yayi Wanka a Kwata Don Murnar Nasarar Buhari

  • Aliyu Muhammad ya tsallake rijiya da baya a 2019, saboda makauniyar soyayya daya samu kansa a ciki ta Shugaba Muhammadu Buhar
  • Biyo bayan sake cin zaɓen da Muhammadu Buhari yayi a shekarar 2019, Aliyu yayi wanka tare da shan kwata mai warin gaske wanda ya Karaɗe ko ina
  • Ya kusa halaka, dakyar aka ceci rayuwar sa bayan tallafin kuɗi daga wasu mutanen kirki, amma yanzu yan APC sun daina ɗaga wayar sa, kuma yayi zargin sun wulaƙanta shi

Bauchi - Aliyu Mohammed Sani wani matashi ne mai matsakaicin shekaru da yayi ƙaurin suna da tashe bayan yayi ninƙaya tare da yin balumi a cikin kwato kwato.

Duk da wannan bajinta da suna da yai, Aliyu yace lokaci yayi da zai kama gabansa, ta hanyar wancakali da tafiyar APC gabaki dayanta.

Kara karanta wannan

25 Sun Mutu, 10 Sunji Munanan Raunuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Bauchi

Ko Menene Yayi Zafi?

APC 2023
Na Fice Daga APC Domin Ta Gama Ɓata Mun Rai-Mutumin da Yasha Kwata Yayi Wanka da ita Don Murnar Nasarar Buhari Hoto: Tribuneonline.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yana da kyau, muyi wa mai karatu tuni da yadda Aliyu ya kusan rasa rayuwar sa a wancan lokacin, sakamakon zuƙar ruwan kwatan da yayi.

Amma saboda taimakon daya samu daga wasu bayin Allah nagari, ya tsallake rijiya da baya sa'ilin da suka ɗauki nauyin maganin nasa.

Tafiya Ta Lula Babu Bayani ga Aliyu

Yanzu shekaru huɗu kenan ga matashin daya kasance mai sana'ar ɗinki.

Duk da dadewar da yayi aka dokin zato, Aliyu yace hakan bazai hana yayi sallama da jam'iyyar ta APC ba tunda dai hakan shine mafi a'ala a gare shi.

Inda yace:

"Duk da kasadar da na ɗauka saboda soyayya ta ga tafiyar jam'iyyar, ba abin da suka saka min dashi sai tarin tulin baƙin ciki".

Aliyu ya shaidawa manema labarai labarin sa maras daɗin ji ga tarin yan jarida da suka haɗu a shelkwatar yan jaridu reshen jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

“Karku Rantsar da Tinubu Domin Yin Hakan Ya Sabawa Dokar Tsarin Mulkin Najeriya” - Baba Ahmed

Yace ya ajiye tafiyar ne ba don komai ba sai don ya cigaba da gudanar da rayuwar sa cikin salama bayan ya shiga halin la-ila-hula'i a kowani bangare na rayuwar sa.

Aliyu Sani da aka fi sani da "Aliyu Gayu Na Baba Buhari" yace biyo bayan ficewar da yayi daga tafiyar Baba Buhari, daga yau ya canja sunan zuwa "Ali na Baba Kauran Bauchi".

Cikin takaici da alamun ƙwalla ya nisa ya ƙara faɗawa jaridar Tribune cewar:

"Sunana Aliyu Muhammed Sani, da akafi sani da Ali Gayu Na Baba Buhari a baya. Domin yanzu kiɗa ya canja, rawa ma zata canja".
"Nine mutumin da mutane suka sani bayan Buhari ya sake cin mulki a shekarar 2019, ta hanyar yin wanka da kwata tare da shan kwatar duk a cikin salon murna."

Yace mutane da yawa sunzo domin jajanta masa, ciki kuwa harda Alhaji Musa Azare wanda ya hau jirgi har zuwa Bauchi don yaga yanayin jikinsa, bayan yasha kwata.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Jihohin da Ba'a Kammala Zaben Gwamna Ba da Waɗanda INEC Ta Dakatar da Tattara Sakamako

Aliyu yace yayi nadama sosai, domin duk tarin magoya bayan APC, da suke da masaniyar abinda yayi babu wanda ya damu dashi kamar Alhaji Musa Azare wanda yake dan jam'iyyar PDP ne. Dalilin da yasa ya zaɓi zama ɗan amutun sa.

"Nayi farin ciki sosai daya zo ya same ni cikin yanayi mai kyau, saboda anyi ta yaɗa raɗe-raɗi cewar na mutu sakamakon shalkwatar da nayi, amma bayan ya tabbatar ban mutu ba, har wani ɗan abu ya kawo ya bani."
"Ni ba cima zaune bane, so nake a ƙarawa sana'a ta jari ko kayan aiki. Bana bukatar kuɗi daga gare ku, ina so ne a ƙara mun karsashi. Nayi jam'iyyar APC ne domin soyayyar da nakewa jam'iyyar". inji Aliyu.

Yace yaje helkwatar NUJ reshen jihar Bauchi ne domin sanarwa da duniya ya canja ɓangaren siyasa zuwa tsagin Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad Kauran Bauchi.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Dan Takarar Gwamnan Kano Ya Cire Rai Tun Kafin a Gama Tattara Sakamako

Aliyu yace ya tuntuɓi masu faɗa aji a jam'iyyar APC, amma babu abinda suke masa sai alƙawarin ƙanzon kurege.

Yace :

"Akwai wani mai taimakawa shugaban ƙasa daga Bauchi, yayi alƙawarin yi mini abin alkairi, amma har yau da nake magana daku, babu abin da yayi mun, ko jinsa ma bana yi, domin ya daina ɗaukar kira na. Na ƙyale shi da Allah".

Ya jaddada cewa, yayi nadamar abinda yayi, da ace an samu rashin sa'a da tuni ya rasa ransa. Sannan yayi kira ga matasa, da kada suyi abinda zasu jefa rayuwar su a halaka domin wani, musamman ma ƴan siyasa.

Aliyu ƙare da faɗin cewa:

"Nayi abin ne cikin rashin sani, babu abinda zaisa nayi irin wannan abu yanzu. bazan taɓa bawa wani shawarar ya aikata irin wannan ɗanyen aiki ba, na godewa Allah da ban mutu ba, wani bazai samu wannan sa'ar ba, don Allah kada ku aikata kuma". Inji Aliyu.

Kara karanta wannan

"Mutuwa Ce Makomar Duk Mai Son Tayar Da Rikici a Ranar Zabe", 'Yan Sanda

Rantsar da Tinubu Ya saɓawa Kundin Tsarin Mulki” Inji Baba Ahmed

Mataimakin Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa daya gabata, Baba Ahmed yayi kira da kakkausar murya akan Shugaban Kotun Koli.

Sannan kiran na Baba Ahmed ya ƙara nausawa kai tsaye wajen Shugaban Ƙasa Buhari akan shima kada ya shiga a aikata abinda ya kira na "Haram".

Baba Ahmed yace, tun kiran nashi ya zama dole domin kuwa APC baya cika ƙa'idar sashi na 134 (2)(a) da kuma (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ke magana akan yadda za'a zaɓi shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel