Gwamna Wike Ya Yaba da Hukuncin Kotun Koli Kan Sauya Fasalin Naira

Gwamna Wike Ya Yaba da Hukuncin Kotun Koli Kan Sauya Fasalin Naira

  • Gwamna Wike ya ce hukuncin Kotun koli ya ɗaure gwamnan CBN, Godwin Emefiele domin ba shi da wani zaɓi
  • Wike, jagoran tawagar G-5 a jam'iyyar PDP, ya nuna goyon bayansa ga matakin tsawaita wa'adin tsoffin naira da Kotu ta ɗauka
  • A cewarsa duk wanda ke da tsohon N200, N500, N1000 ya ci gaba da kashe kayansa cikin kwanciyar hankali

Oyo - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, a ranar Jumu'a, ya goyi bayan hukuncin Kotun koli wanda ya tsawaita wa'adin amfani da tsohon naira N200, N500 da N1000 zuwa 31 ga watan Disamba.

Wike ya ɗaure gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, inda ya ce ba shi da wani zaɓi illa yin biyayya ga umarnin Kotu mai daraja ta ɗaya.

Gwamnan CBN da Wike
Gwamna Wike ya aika sako ga gwamnan CBN Hoto: CBN
Asali: Facebook

Channels tv ta rahoto Wike na cewa:

Kara karanta wannan

Shin Tsoffin N500 da N1000 Zasu Ci Gaba da Amfani Bayan Hukuncin Kotun Koli? Sabbin Bayanai Sun Fito

"Na gode Allah yau Kotun koli ta gaya masu tsohon kuɗi zasu ci gaba da amfani har zuwa karshen Disamba. Saboda haka idan kuna da tsoffin takardun kuɗi, ku kashe su inji Kotu mafi girma a kasar nan."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Abun ya fi karfin gwamnan babban bankin Najeriya, ba shi da wani zaɓi saboda babu wani umarni da zai warware hukuncin Kotun koli."

Gwamna Wike ya yi wannan jawabin ne lokacin da yake kaddamar da wasu muhimman ayyuka a jihar Oyo jim kaɗan bayan Kotun koli ta yanke hukuncin karshe ranar Jumu'a

Ya kaddamar da gidan sayar da man jiragen sama mai girman lita 5,000,000 a filin jirgin Ibadan. Wike ya yi kira da a kafa mulkin jamhuriya na gaskiya kuma a sauya fasalin kasa.

A cewar gwamna Wike, da yawan albarkatun kasa jihohi ya kamata su rika tafiyar da su ba gwamnatin tarayya ba, kamar tadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ci gaba da kashe tsoffin Naira: Bankuna sun yi magana bayan hukuncin kotun koli

Bugu da ƙari ya bukaci gwamnatin tarayya ta biya kudin da jihar Oyo ta kashe a aikin gidan man jirgin ko kuma ta damƙa shi hannun gwamnantin Seyi Makinde.

CBN Ya Yi Gum Game da Hukuncin da Ƙotun Koli Ta Yanke Kan Sauya Naira

A wani labarin kuma Wasu bayanai sun fito daga CBN bayan hukuncin Kotun koli kan sauya fasalin naira.

Har kawo yanzu babban bankin bai fidda sanarwa a hukumance ba game da batun amfanin tsoffin takadun naira uku da aka sauya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel