CBN Ya Yi Gum Game da Hukuncin da Ƙotun Koli Ta Yanke Kan Sauya Naira

CBN Ya Yi Gum Game da Hukuncin da Ƙotun Koli Ta Yanke Kan Sauya Naira

  • Har yanzun babban bankin Najeriya CBN bai ce uffan ba a hukumance game da hukuncin Kotun koli
  • Wani ma'aikacin CBN ya bayyana cewa bankin yana bin doka sau da kafa da ƙarin umarni daga bangaren masu zartaswa
  • Wani Farfesa a jami'ar jihar Nasarawa ya shawarci CBN ya yi biyayya ga hukuncin Kotu lamba ɗaya

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya yi gum bai ce komai ba har zuwa yanzun bayan Kotun ƙoli ta umarci a ci gaba da hada-hada da tsoffin takardun N200, N500 da N1000 har zuwa 31 ga watan Disamba, 2023.

Shin CBN zai yi ɗa'a ga umarnin Ƙotu?

Wani ma'aikacin CBN, wanda ya amince ya zanta da The Natiion kan batun bisa sharadin boye bayanansa, ya ce babban banki yana aiki ne bisa sahalewar bangaren zartaswa.

Kara karanta wannan

"Ta Karewa Emefiele" Gwamna Wike Ya Maida Martani Jim Kaɗan Bayan Hukuncin Kotun Koli Kan Naira

Tsarin sauya fasalin naira.
Sabbin takardun kuɗi da gwamnan CBN, Godwin Emefiele Hoto: CBN
Asali: UGC

Ma'aikacin ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"CBN yana bin doka sau da ƙafa kuma wani ɓangare ne da ke gudanar da harkokinsa karkashin sahalewar sashin zartaswa na gwamnati."

Wannan kalamai na nufin CBN ka iya wanke hannunsa ya miƙa nauyin jawabi kan batun sauya fasalin naira zuwa hannun gwamnatin tarayya.

Yayin da aka tambaye shi ko hukuncin Kotun ƙoli na nufin dakile tsarin CBN na takaita hada-hadar kuɗi a hannu, ma'aikacin ya ci gaba da cewa:

"Da wahala hakan ta faru saboda dama can akwai tsarin kuma yana aiki tun shekarar 2012."

Biyayya ga hukuncin Kotu zai taimaka wa al'umma

Da yake martani kan hukuncin da Kotun koli ta yanke ranar Jumu'a, 3 ga watan Fabrairu, 2023, Farfesa Uche Uwaleke, na jami'ar jihar Nasarawa ya shawarci CBN da cewa:

"Ya kamata ya yi ɗa'a ga umarnin Kotun koli tun da hukuncin ya fito ne daga Kotu mai daraja da ɗaya a ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Hukuncin da Kotun ƙoli ta Yanke Na Canjin Fasalin Kuɗi Zai Kasance Kyakkyawan Tushe Ga Mulkin Tinubu — Yahaya Bello

"Idan aka aiwatar da hukuncin zai farfaɗo da harkokin tattalin arzikin da suka durƙushe kuma ya rage raɗaɗin wahala da kuncin rayuwa wanda tsarin ya jefa 'yan Najeriya a ciki."

Legit.ng Hausa ta tuntuɓi wani ma'aikacin banki don jin ci gaban da aka samu, ya ce dama suna karban tsohon kuɗi daga kwastomominsu tun kafin hukuncin Kotu.

"Dama muna amsar tsohon kuɗi daga hannun mutane idan sun cike Fam, amma bayan hukuncin Kotu, bamu sani ba ko CBN zai umarci mu rika baiwa mutane tsohon N500, N1000."

Aminu Aminu Majeh, wani mai sana'ar POS a jihar Jigawa, ya shaida wa wakilin mu cewa tuni harkokin kasuwancinsu ya tsaya cak domin babu isassun tsabar kuɗi.

Ya ce ba su zauna haka nan ba, suna kokarin nemo takardun kuɗin su baiwa kwastomomi amma saboda wahala dole suka kara kuɗin caji.

"Muna maraba da hukuncin Kotu, muna fatan CBN da FG zasu yi abinda ya dace, su tausayawa mutane," inji shi.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Yunwa Da Hare-Hare Yasa Sun Koma Sace Mutane Tare Da Neman Kudin Fansa

A wani labarin kuma Gwamna El-Rufai Ya Fallasa Yadda Minista Ya Yaudari Buhari, Aka Canza Takardun Kudi

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya zargi gwamnan CBN da kawo tsarin sauya fasalin naira domin naƙasa jam'iyyar APC da taimaka wa PDP.

El-Rufai ya bayyana yadda babban lauyan gwamnati ya ta ya Emefiele suka ja hankalin Buhari kan abinda ba'a taɓa yi ba duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel