Bankunan Najeriya Sun Yi Magana Kan Hukuncin Kotun Koli Na Ci Gaba da Kashe Tsoffin Kudi

Bankunan Najeriya Sun Yi Magana Kan Hukuncin Kotun Koli Na Ci Gaba da Kashe Tsoffin Kudi

  • Manyan jami’an bankuna a Najeriya sun ce suna jiran martanin CBN game da umarnin kotun koli kan ci gaba da kashe tsoffin kudi
  • Sun ce ba sa amsa umarni ne daga kotun na koli, suna karbar umarni ne daga babban bankin kasa na CBN
  • CBN kuwa, har yanzu bai yi martani ga hukuncin da kotun kolin ya yanke a ranar Juma’a 3 ga watan Maris ba

Kotun kolin Najeriya ya yi wasti da umarnin CBN ga bankunan kasar nan na daina amfani da tsoffin kudin N200, N500 da N1000 a kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, kotun koli a ranar Juma’a 3 ga watan Maris, 2023 ta ce za a ci gaba da kashe tsoffin kudaden da aka sauya a kasar.

A hukuncin da kotun ya yanke tare da alkalansa bakwai, ya ce ‘yan Najeriya za su iya ci gaba da kashe kudaden har zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Hukunci 6 da Kotun Koli ta Zartar Game da Tsarin Canza Takardun Kudi a Najeriya

Batun sabbin kudi da bankunan kasa
Sabbin kudin Najeriya da ke ci gaba da jawo cece-kuce | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Wannan na nufin cewa, za a ci gaba da kashe tsoffin kudaden tare da sabbin da aka buga a watan Disamban bara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba a yi daidai ba wajen kawo dokar kudi

Kotun kolin ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kuskuren amincewa da kawo karshen amfani da tsoffin kudaden ba tare da yin shawari da masu ruwa da tsaki ba.

Mai shari’a Emmanuel Agim na kotun ya zargi Buhari da kin bin umarnin doka kan wannan yunkuri na sauyin kudi da daina afami da tsoffi.

Ma’aikatan bankuna sun magantu

Sai dai, wasu manyan ma’aikatan bankunan da suka zanta da Legit.ng kuma suka nemi a sakaya sunayensu saboda tsaro sun ce CBN ne zai yi magana su saurara.

Wani daga cikin ma’aikatan bankin Eco ya ce, za su bi umarnin CBN ne ba wai abin da kotun kolin ya fada ba.

Kara karanta wannan

Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu

Ya ce:

“Cibiyoyin hada-hadar kudi a Najeriya a tsare suke, kuma muna sauraran abin da CBN yace ne kadai. Duk da hukuncin, muna bukatar ji daga masu tsara mana komai.”

Da aka tambaye shi ko babban bankin zai bi umarnin kotun, ya ce CBN na amsa umarnin shugaban kasa ne kan lamari irin wannan.

Hakazalika, wani ma'aikacin bankin Unity a jihar Gombe da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Dole CBN ne za ta bamu batun karshe da za mu bi. Aimka ga abin da ya faru a hukuncin kotun na 15 ga ga watan Faburairu. Maganar CBN muka bi. To wannan ma idan CBN bai lamunce ba haka ne."

Kokarin da muka yi don jin ta bakin mai magana da yawn CBN, Isa Abdulmumini bai samu samu ba.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da samun matsaloli game da karancin sabbin kudi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Kotun koli ya ce ya kamata a yi gyara a kudin tsarin mulkin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel