Karya Ne, Mu Dahiru Bauchi Yake Goyon Baya: APC Ta Saki Bidiyon Shehi

Karya Ne, Mu Dahiru Bauchi Yake Goyon Baya: APC Ta Saki Bidiyon Shehi

  • Jam'iyyar APC ta yi martani kan labarin cewa babban shehin addinin Musulunci ya ce Atiku zai zaba
  • Kwamitin kamfe tace ai tuni Sheikh Dahiru Bauchi yayi addu'an Allah ya baiwa Tinubu da Shettima Nasara
  • Yan siyasan Najeriya na cigaba da neman wadanda zasu mara musu baya ana yan kwanaki zabe

Kwamitin yakin neman zaben Jam'iyyar All Progressives Congress APC tayi martani game da labarin cewa babban Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, ya sanar da goyon bayansa ga Atiku Abubakar.

Kwamitin ya ce dan takarar shugaban kasansu, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, Shehi ya fara yiwa addu'a kuma ya tofawa albarka.

Kwamitin ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita inda aka saki bidiyon Sheikh Dahiru Bauchi yana addu'a wa Shettima da Asiwaju.

Dahoru
Karya Ne, Mu Dahiru Bauchi Yake Goyon Baya: APC Ta Saki Bidiyon Shehi
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Babangida Ya Fito Ya Yi Maganar Zabe da Nasarar Tinubu

A faifan bidiyon, an ga Shettima yayi durkuso gaban Shehi yana neman tabarruki.

Shehi kuma yayi addu'an Allah ya baiwa Tinubu da Shettima nasara.

Kalli bidiyon:

Shugabancin Kasa Na 2023: Tinubu Ya Aika Sako Mai Muhimmanci Ga Shugabannin Addini Gabanin Zabe

A wani labari, Ɗan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dau alkawarin kamanta adalci tare da bayarda nagartaccen shugabanci idan Allah ya bashi damar zama shugaban Najeriya a 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin zantawa ta musamman da yayi da malamai da shugabannin addinin musulunci da suka fito daga yankin arewa maso gabas da Legit.ng ta samu da Abdulaziz Abdulaziz na ofishin watsa labaran Tinubu ya fitar a ranar Litinin 23 ga watan Janairu.

Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya ce hakan zai zurfafa hadin kai da samun ribar dimokradiyya tsakanin yan Najeriya a yayin da ake fuskantar zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel