Fusatattun Kiristoci a Neja Sun Yi Aikin Dana-Sani, Sun Kone Ofishin Yanki Na ’Yan Sanda

Fusatattun Kiristoci a Neja Sun Yi Aikin Dana-Sani, Sun Kone Ofishin Yanki Na ’Yan Sanda

  • Wasu fusatattun kiristoci a jihar Neja sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta bayan mutuwar wani rabaran
  • Rahoto a baya ya bayyana yadda 'yan bindiga suka kone wani malamin coci da ransa, ya mutu nan take
  • An sake samun hargitsi bayan da aka zo yiwa malamin addu'a, an hallaka mutum daya nan take

Paiko, jihar Neja - Matasa da mata a jihar Neja sun dauki doka a hannu yayin da suka kone ofishin ‘yan sandan yanki da ke Kafin-Koro a karamar hukumar Paiko a jihar.

Wannan lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata 17 ga watan Janairun 2023 kamar yadda rahotanni suka bayyana, The Nation ta ruwaito.

Kwanaki uku kafin haka, wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki wani coci, inda suka kone wani rabaran fada mai suna Isaac Achi na cocin Katolikan St. Peter and Paul da ke Kafin-Koro, lamarin da ya kai ga mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Halaka Magidanci Tare da Sace Yaransa 2 a Farmakin da Suka Kai FCT

An kone ofishin 'yan sanda a Neja
Fusatattun Kiristoci a Neja Sun Yi Aikin Dana-Sani, Sun Kone Ofishin Yanki Na ’Yan Sanda | Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

Da sanyin safiya kusan karfe 7 na ranar Talata, mambobin cocin Katolikan da suka hada mata, wasu kuma da coci ECWA sun taro a wurin da lamarin ya faru domin yiwa rabaran din addu’o’i.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

'Yan sanda sun zo ba da kariya, mambobin coci sun tada hankali

Sai dai, an ga tarun jami’an tsaro a wurin da lamarin ya faru, wadanda aka ce sun zo ne daga ofishin yanki na Kafin-Koro domin ba mutanen tsaro, Within Nigeria ta ruwaito.

Da suke ci gaba da jin zafin mutuwar malaminsu, mata a wurin sun yi amincewa da kariyar ‘yan sandan, inda suka nemi su gaggauta barin wurin kasancewar sun gaza taimakawa rabaran din.

Sun kuma zargi ‘yan sandan da rashin tabuka komai wajen kare rabaran Achi, daga suka nemi su bar wurin.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Yan Bindiga Suka Halaka Amarya da Ango Yan Kwanaki Kafin Aurensu

Hargitsi ya tashi, 'yan sanda sun harbi mutum 1

Domin watsa taron, ‘yan sandan sun yi harbin iska, lamarin da ya kai ga mutuwar wani matashi nan take.

Hakan ya jawo hargitsi, har ta kai ga aka fara zanga-zanga da dauki ba dadi da ‘yan sandan.

A cikin wannan yanayin ne wasu mutane daga cikin kiristocin suka bankawa ofishin ‘yan sandan wuta nan take ya kone kurmus.

Ya zuwa yanzu dai bamu samu jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A baya kunji yadda 'yan ta'addan suka kone malamin coci kurmus a jihar Neja, lamarin da ya kawo cece-kuce a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel