Abokin Takarar Tinubu Ya Nuna Matsayarsa, Ya Gargadi Mutane a Kan ‘Dan Takaran APC

Abokin Takarar Tinubu Ya Nuna Matsayarsa, Ya Gargadi Mutane a Kan ‘Dan Takaran APC

  • Alamu sun nuna Fasto Tunde Bakare ba zai goyi bayan Bola Tinubu a zaben shugaban kasa ba
  • Limamin cocin Citadel Global Community ya ankarar da al’umma a game da wanda za su zaba
  • Bakare yace bai dace ‘dan siyasa ya kauracewa tambayoyi ko ya dage cewa dole okacinsa ya yi ba

Lagos - Fasto Tunde Bakare mai jagorantar cocin Citadel Global Community ya yi wani jawabi, da ake ganin ya soki ‘dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu.

A ranar Lahadi, 15 ga watan Junairu 2023, Daily Trust ta rahoto Faston yana cewa bai kamata ‘yan siyasa su bukaci wasu su amsa tambayoyin da aka jefa masu ba.

Duk da bai kama suna ba, Legit.ng Hausa ta na zargin Tunde Bakare yana magana ne kan Tinubu lokacin da ya yi magana a dakin taron Chatham House a Birtaniya.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Wadanda Zai ba Mukamai da Abin da Zai Yi Kafin Kwana 100 a Aso Rock

Malamin addinin ya gargadi mutane a kan salon siyasar bani-na-iya da wasu suke yi a yau.

Bakare ya yi kira ga mutanen Najeriya da su guji zaben ‘dan siyasar da zai raba masu kudi a zaben da za ayi, ya ce kyau a maida hankali a kan cigaban Najeriya.

This Day ta rahoto cewa Fasto Tunde Bakare ya soki taken ‘Emi lokan’ wanda Bola Tinubu mai neman mulki a APC ya fito da shi da sunan lokacinsa ya yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu
Taron yakin neman zaben APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

A wata gabar, Bakare wanda ya sha kashi a zaben tsaida gwani na APC ya zargi wasu ‘yan takara da kauracewa muhawara tare da kin yi wa jama’a bayani.

Idan aka tafi a haka, zai zama ‘dan siyasa yana mulki ne ba saboda cigaban mutanen da yake jagoranta ba, Bakare yana ganin abin ya zama cin ma burinsa.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Yadda Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi Za Suyi Yaki a Kan Kuri’un Kano

Bakare wanda ya nemi mataimakin shugaban kasa a inuwar CPC a 2011 ya ce ana bukatar masu neman mulki su rika yi wa talakawa bayanin inda aka dosa.

A cewar Bakare, daga cikin abin da ake bukata wajen ‘dan siyasa na kwarai akwai kaudawa al’umma tsoro da dar-dare da ke tare da su, da sa masu rai.

Haka zalika Bakare ya ce dole a rika tafiya da kowa; mata, matasa, dattawa da masu nakasa.

Manufofin Bola Tinubu

A baya aka rahoto Asiwaju Bola Tinubu yana cewa a kwanaki 100 na farko a mulki zai jawo kwararru domin ya canza fasalin tattalin arzikin kasar nan.

Gwamnatin Tinubu za ta taimakawa marasa galihu, sannan ta gina gidaje masu araha, asibitoci da makarantun zamani, amma idan ta cire tallafin fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel