Dubai Ta Cire Haraji Kan Barasa, Ta Ba da Damar Kwankwadarta a Watan Ramadana

Dubai Ta Cire Haraji Kan Barasa, Ta Ba da Damar Kwankwadarta a Watan Ramadana

  • Birnin Dubai ya cire dokoki da haraji kan barasa domin ba bakin kasashen wajen damar shiga su hole a kasar
  • Hakazalika, Dubai ta amince ake shan barasa da rana a watan Ramadana, sabanin yadda dokar take a baya
  • An san Dubai da saukaka dokokinta masu tsauri saboda jan hankalin baki 'yan kasashen waje, musamman Turai

Dubai, UAE - Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ce ta cire harajin da ke kan barasa har kaso 30% domin habaka kofar bude ido a kasar, rahoton CNBC.

Kasar fitacciya a kasuwanci ta kuma bayyana dage dokar neman lasisin shan giya ga daidaikun mutane, wanda a da dukkan baki ke bukatar nema kafin kwankwadar barasa.

Tun lokacin Korona, Dubai dai na ci gana da saukaka dokokin siyarwa da shan barasa a kasar, kuma a yanzu an amince a siyar kana a sha giya a cikin watan Ramadana da rana.

Kara karanta wannan

Kaico: Shugaban Ukraine ya gano shirin da Rasha ke yi na son wargaza kasarsa

Hakazalika, kasar ta ba 'yan kasuwa damar karbar kayayyakin da suke da alaka da barasa zuwa cikinta.

Dubai ta amince a yi marisa a Ramadana, an dage haraji kan barasa
Dubai Ta Cire Haraji Kan Barasa, Ta Ba da Damar Kwankwadarta a Watan Ramadana | Hoto: Kaveh Kazemi / Contributor
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan yunkuri na Dubai ba komai bane face shirin sake sanya kasar ta zama abar sha'awa a idon masu bude.

Kamfanonin shigo da barasa kasar, Maritime and Mercantile International (MMI) da African & Eastern sun bayyana cewa, wannan yunkuri na Dubai zai nuna a farashin barasa a kasar.

A cewar MMI:

"Wadannan ka'idojin da aka gyara kwanan nan kayan aiki ne na ci gaba da tabbatar da aminci da alhakin saye da shan barasa a Dubai da ma UAE."

A cewar wani rahoton BBC, wannan dokar ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Janairun 2023, kuma za a sake duba ta bayan shekara daya.

Baki sun fi 'yan kasa yawa a Dubai

A cewar rahoto, baki 'yan kasashen waj sun yi adadin mutanen da asalinsu 'yan kasar ne, kuma sukan yi tafiya ne mai tazara har zuwa Umm al-Quwain domin saye da kwankwadar barasa.

Kara karanta wannan

2022: Jerin kasashe 64 da Najeriya ta siyo man ferur din N1.2trn a cikin watanni 3 kacal

Birnin na ci gaba da jawo baki 'yan kasar waje domin yi aiki saboda bayyana kasar a matsayn kasar 'yanci kuma mai kwaikwayon rayuwar Turawan yamma.

A yanzu dai birnin Dubai na ci gaba da samun karuwar gasar gogayya da sauran birane masu tasowa a yankin Larabawa.

A dawo batun doka, an ce an amince wanda ba Musulmi ba da ya kai shekaru 21 ya sha, ya yi safara ko adana barasa, kuma dole ya samu lasisi daga 'yan sanda.

A Najeriya, akwai wasu jihohi 10 da mata suka fi shan barasa, rahoto ya bayyana adadin jihohi da sunayensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel