Kasar Rasha Na Shirin ‘Wargaza’ Kasa Ta, Inji Shugaban Ukraine Zelensky

Kasar Rasha Na Shirin ‘Wargaza’ Kasa Ta, Inji Shugaban Ukraine Zelensky

  • Kasar Ukraine ta bayyana tsoronta ga yadda kasar Rasha ke shirin kawo mata sabbin hare-hare a 'yan kwanakin nan
  • An ce kasar Rasha ta siyo manyan makamai daga kasar Iran, kuma a haka ne za ta kai hari don wargaza kasar
  • An fara fada tsakanin Ukraine da Rasha tun a wata Fabrairu, ana kare jini biri jini tsakanin kasashen biyu

Kyiv, Ukraine - Kasar Rasha na shirin kai munanan hare-haren kan kasar Ukraine a ‘yan kwanakin nan masu zuwa, a cewar shugaba Zelensky na kasar ta Ukraine.

A cewarsa, Rasha za ta yi amfani da wasu nau’ikan kananan jirage marasa matuka don aiwatar a shirin wargaza kasar ta Ukraine mai makwabtaka da Rasha.

A cewar Zelensky, ya samu bayanan sirri daga Rasha kan wannan shiri na hare-hare, kuma kasar Iran ne ta kera jiragen da Rashan za ta yi amfani dasu, inji rahoton BBC Hausa.

Kara karanta wannan

2023: Sunaye da Gudumawar da Mutum 7 Zasu Bayar Wurin Canza Fasalin Najeriya

Rasha na son wargaza Ukraine, inji Zelensky
Kasar Rasha na shirin 'waraza' kasa ta, inji Shugaban Ukraine Zelensky | Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ukraine ta yi ikrarin hallaka sojojin Rasha

Idan baku manta ba, kasar Ukraine ta yi ikrarin kai hari kan dakarun Rasha a yankin Donbas, inda tace ta kashe daruruwansu a sabon harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A gefe guda, Rasha ta musanta wannan ikrari tare da cewa, an kashe dakarunta 63 ne kacal a wannan harin, NDTV ta tattaro.

A sabon batunsa, Zelensky ya koka da cewa, Rasha na shirin ‘wargaza’ Ukraine a sabbin hare-haren da take da shirin kaiwa kasar.

Ya bayyana wannan zargin ne a birnin Kyiv a daren jiyar Litinin 2 ga watan Janairu yayin da yake magana da duniya baki daya.

Ana ci gaba da samun munanan hare-hare daga kasar Rasha a kan Ukraine a ‘yan kwanakin nan, musamman kan wasu tashoshin lantarkin kasar ta hanyar amfani da jirage marasa matuka.

Kara karanta wannan

Ashe babu dadi: Kasurgumin dan bindiga ya firgita, an rusa gidansa, an kashe yaransa 16

Kasashen Ukraine da Rasha sun yi jimamin rashin sojoji da fararen hula tun bayan fara wannan yaki da ya dauki kusan shekara ana tafkawa.

An dawo da gawar dan Afrika da aka kashe garin taya Rasha yakar Ukraine

A wani labarin kuma, wani matashi dan kasar Zambia ya rasa ransa a yakin da ake tsakanin Rasha da Ukraine.

Bayan mutuwa a filin daga, an tattaro gawarsa domin dawo da ita kasarsu, an yi bikin karbarsa a kasarsu.

Rahoto ya bayyana yadda aka kai matashin filin daga don taya kasar Rasha yaki da Ukraine a watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel