Jerin Kasashe 64 da Najeriya Ta Shigo da Man Fetur Dinsu Yayin da NNPC Ta Siya Man N1.2trn a Cikin Wata 3

Jerin Kasashe 64 da Najeriya Ta Shigo da Man Fetur Dinsu Yayin da NNPC Ta Siya Man N1.2trn a Cikin Wata 3

 • Wani sabon rahoto ya bayyana cewa, kamfanin man fetur na Najeriy ya kashe sama da N1.2trn wajen shigo da man fetur a watanni uku kacal
 • An shigo da wannan man fetur ne daga kasashen waje da suka hada da jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Najeriya
 • A ‘yan kwanakin baya da suka wuce, ‘yan Najeriya sun shaida tsada da karancin man fetur a gidajen man kusan dukkan sassan kasar

Hukumar kididdiga ta NBS ta bayyana cewa, Najeriya ta kashe N1.199trn wajen shigo da man fetur a cikin watanni uku na tsakiyar shekarar da ta gabata; 2022 (tsakanin Yuli zuwa Satumba)

NBS ta bayyana hakan ne a cikin kididdigar harkalla da kasashen waje da Najeriya ta yi a kwata na uku na shekarar 2022 da ta kare, kamar yadda Legit.ng ta tattaro a shafin hukumar na yanar gizo.

Kara karanta wannan

An so a ci banza: 'Yan crypto sun sharbi kuka a 2022, an fadi jerin kudaden da suka karye

A cewar rahoton, kudaden da aka kashe wajen shigo da mai tsakanin Yuli da Satumban bara ya kai karin 16.2% idan aka kwatanta da N1.026trn na kudaden da aka siyo irin wadannan kaya a shekarar 2021.

Najeriya ta kashi N1.2trn wajen siyo man fetur a kasashen waje
Jerin Kasashe 64 da Najeriya Ta Shigo da Man Fetur Dinsu Yayin da NNPC Ta Siya Man N1.2trn a Cikin Wata 3 | Hoto: NBS
Asali: Facebook

NBS ta kuma bayyana cewa, kudurin kwata na uku na 2022 na shigo da man fetur ya kasance mafi girma a ‘yan shekarun da suka gabata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A irin wadannan kwata na uku a shekarun 2018, 2019 da 2020, an kashe N883.565bn, N371.8bn da N532.615bn bi da bi na shigo da man fetur.

Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ne kadai ke shigo da man fetur daga wasu kasashen waje a Najeriya.

Kayayyakin da aka fi shigo dasu Najeriya

Gaba dayan kayayyakin waje da Najeriya ta shigo dasu a kwata na uku a 2022 sun kai na jumillar kudade N5.66trn.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Gwamna Wike Ya Sake Tona Wani Babban Sirrin Atiku

NBS ta bayyana cewa, man fetur ne a kan gaba a jerin kayayyakin da aka shigo dasu Najeriya a cikin wadancan watanni uku, daga shi sai man gas da aka shigo da na N261.595.

Alkama kuwa ta cinye N252.621bn, kuma itace ta uku daga jerin kayayyakin da aka shigo dasu Najeriya watannin uku.

Jerin kasashen da aka shigo da man fetur daga garesu

NBS bata bayyana daga wasu kasashe ne Najeriya ta shigo da man fetur ba, amma wani rahoton WITS ya nuna kasashen da Najeriya ke harkallar man fetur dasu kamar haka:

 1. United Arab Emirates
 2. Austria
 3. Belgium
 4. Benin
 5. Bulgaria
 6. Canada
 7. Switzerland
 8. Chile
 9. China
 10. Cote d'Ivoire
 11. Germany
 12. Denmark
 13. Egypt, Arab Rep.
 14. Spain
 15. Estonia
 16. Ethiopia(excludes Eritrea)
 17. Finland
 18. France
 19. Gabon
 20. United Kingdom
 21. Ghana
 22. Guinea
 23. Equatorial Guinea
 24. Greece
 25. Hungary
 26. Indonesia
 27. India
 28. Ireland
 29. Iraq
 30. Israel
 31. Italy
 32. Japan
 33. Korea, Rep.
 34. Kuwait
 35. Lebanon
 36. Sri Lanka
 37. Lithuania
 38. Luxembourg
 39. Latvia
 40. Morocco
 41. Mexico
 42. Malaysia
 43. Niger
 44. Nicaragua
 45. Netherlands
 46. Norway
 47. Other Asia, nes
 48. Pakistan
 49. Poland
 50. Korea, Dem. Rep.
 51. Portugal
 52. Romania
 53. Russian Federation
 54. Saudi Arabia
 55. Singapore
 56. Sweden
 57. Eswatini
 58. Togo
 59. Thailand
 60. Tunisia
 61. Turkey
 62. United States
 63. Vietnam
 64. South Africa

Kara karanta wannan

Shekarar 2022 Ta Zama Shekarar Zulumi Da Fargaba, Akalla Mutum 8,000 Ne Suka Rasa Ransu a Shekarar

A kullum gwamnatin Najeriya na bayyana yunkurin dakile wahalar mam fetur a kasar, amma abin bai kai wa ga nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel