Yadda Janar Obasanjo Ya Tsiyace Shekaru 3 Bayan Ya Sauka daga Karagar Mulki

Yadda Janar Obasanjo Ya Tsiyace Shekaru 3 Bayan Ya Sauka daga Karagar Mulki

  • A lokacin da Janar Olusegun Obasanjo ya bar fadar Shugaban kasa a 1979, bai da wasu makudan kudi
  • A tarihin tsohon shugaban Najeriya wanda Musikilu Mojeed ya rubuta, aka fahimci abin da ya faru a 1982
  • Duk da ya rike mulkin kasa a lokacin Soja, sai da ta kai Obasanjo yana neman aron kudin da zai rike gonarsa

Ogun - A Oktoban shekarar 1979, Janar Olusegun Obasanjo ya bar kujerar shugaban kasa na mulkin soja, amma kafin tafiya tayi nisa, kusan sai ya tsiyace.

Premium Times tace Olusegun Obasanjo ya bada labarin yadda ya karbi bashi banki domin ya kula da tafiyar da gonarsa da ke garin Ota a jiharsa ta Ogun.

Musikilu Mojeed shi ne Editan ya da ya rubuta littafin tarihin tsohon shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaba Buhari Ya Yi Kwanaki fiye da 200 a Asibiti, Ya Ziyarci Kasashe 40

A shafi na 31 na littafin, an ji yadda Janar Obasanjo ya ci bashi daga bankin United Bank of Africa, ya kafa gonarsa, amma daga baya ya gaza kula da ita.

Bayan shekaru 3, Obasanjo na neman bashi

Zuwa shekarar 1982, Obasanjo bai da kudi, ya garzaya neman aron N80, 000 daga wajen tsohon Gwamnan sojan yamma ta tsakiya, Samuel Ogbemudia.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Marubucin littafin yake cewa takardun da ya samu sun nuna masa Obasanjo bai bar karagar mulki da tarin dukiya ba, duk da ya yi shekaru uku a mulki.

Janar Obasanjo
Olusegun Obasanjo da Jimmy Carter Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images
"A ranar 7 ga watan Mayu 1982, ya aikawa abokinsa Samuel Ogbemudia takarda yana mai rokon ya ci bashin kudi N80, 000.
A wasikar, ya bayyana halin tattalin arzikinsa a cikin matsin lamba, ya nemi Janar din ya ba shi aro domin kula da gonarsa."

Kara karanta wannan

Shinkenan ta takewa Tinubu, 'yan jiharsa su bayyana dan takarar da za su zaba ba shi ba

- Musikilu Mojeed

"Kayi hattara da 'yan kasuwa"

Abin ban mamaki, Janar Obasanjo a lokacin yana gidan soja, ya taba rubutawa Ogbemudia takarda, yana gargadinsa ya yi hattara da alaka da attajirai.

Rahoton yace an yi haka ne a lokacin yakin basasa a watan Yulin 1969, sa'ilin Obasanjo yana jagorantar rundunar 3rd Marine Commando a Fatakwal.

Yayin da Najeriya ta barke da yakin basasa na Biyafara, shi Birgediya Ogbemudia yana kan kujerar Gwamnan jihar Yamma ta tsakiya da aka kirkira a 1963.

Wahalarmu da Gwamnoni - Atiku Abubakar

An i labari cewa ‘Dan takaran Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya gaskata abin da Mai girma Muhammadu Buhari ya fada kan Gwamnoni.

Atiku Abubakar ya bada labarin irin takaddamar da suka fuskanta da Gwamnonin kasar bayan sun yi yunkurin ba kananan hukumomi kudinsu kai-tsaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel