Atiku Abubakar Ya Tona Wadanda Suka Kawo Masu Cikas a Lokacin Mulkin Obasanjo

Atiku Abubakar Ya Tona Wadanda Suka Kawo Masu Cikas a Lokacin Mulkin Obasanjo

  • Atiku Abubakar yace Gwamnoni ba su amaince a rika aikawa kananan hukumomi kudinsu kai-tsaye ba
  • ‘Dan takaran Shugaban kasa a jam’iyyar PDP yace Gwamnonin jihohi sun kawo masa tasgaro a ofis
  • Atiku yace akwai matsala a dokar kasa, don haka ake dauke abin da kananan hukumomi suka mallaka

Lagos - Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP, ya bada labarin rigimarsu da Gwamnonin jihohin kasar nan.

Alhaji Atiku Abubakar ya yi wannan bayani ne yayin da ya halarci zaman da gidan talabijin Arise TV ya shirya da masu neman shugabancin Najeriya.

‘Dan takaran na PDP yace a lokacin mulkinsu, Gwamnonin jihohi suka hana a rika aikawa kananan hukumominsu kudinsu kai-tsaye da sunan doka.

Muhammadu Buhari ya yi gaskiya

The Cable tace Atiku Abubakar ya yarda da abin da Mai girma Muhammadu Buhari yake fada a kan gwamnoni da ke lakume kudin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Satar Kudin Kananan Hukumomi: Gwamnan Kudu Mai Karfin Fada A Ji Ya Gargadi Buhari

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku yace a lokacin da suka karbi mulki a 1999, sun yi kokarin farfado da kananan hukumomi, amma Gwamnonin da ke mulki, suka ce ba su yarda ba.

"A lokacin da na shiga ofis a 1999, kananan hukumomi aka damka mani, sai na ba Akanta Janar umarni cewa a rika aika masu kudinsu kai-tsaye.
Bayan an dabbaka wannan tsari na watanni tara, sai Gwamnoni suka fara yin bore, suna cewa wannan hakan ya sabawa kudin tsarin mulkin kasa.
Saboda haka sai muka duba tsarin mulki, muka ga an ce akwai bukatar a samu wani asusun hadaka, inda za a rika tura kudin kananan hukumomi
A nan kuma gwamnatin jiha za ta zuba wani kaso na kudin da aka tatsa a cikin asusun. - Atiku Abubakar

Nan fa daya!

Herald ta rahoto Atiku yana cewa inda matsalar take ita ce ta yadda hukumomi za su cire kudi daga akawun din, a haka gwamnoni suka wawure dukiyar.

Kara karanta wannan

Daya Bayan Daya, Gwamnoni Suna Maidawa Buhari Martanin Zargin da Yayi Masu

A wancan lokaci, ‘dan takaran yace gwamnonin sun bada uzurin gina jami’o’in jiha, suka yi ta taba kudin asusun hadakar, har ta kai yanzu kudin sun kare.

An yi wa Gwamnoni kudin goro?

Shugaban kasa ya zargi wasu Gwamnoni da wawurar dukiyar kananan hukumomin da ke kasansu. Amma an ji labari wasu jihohi sun shiga maida martani.

Gwamna Dopo Abiodun, David Umahi, Solomon Lalong, da Nyesom Wike da wasunsu, sun nuna ba su taba asusun kananan hukumomin da ke kasansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel