Daya Bayan Daya, Gwamnoni Suna Maidawa Buhari Martanin Zargin da Yayi Masu

Daya Bayan Daya, Gwamnoni Suna Maidawa Buhari Martanin Zargin da Yayi Masu

  • Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wa Gwamnoni kudin goro, yace suna taba kudin kananan hukumomi
  • Wannan ya jawo Gwamnonin jihohi suna ta fitowa domin su nesanta kansu daga laifin da aka jefe su da shi
  • David Umahi, Solomon Lalong, da Nyesom Wike da wasunsu, sun nuna ba su taba asusun kananan hukumomi

Abuja – Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zargi Gwamnonin jihohi da taba dukiyar kananan hukumominsu, hakan ya jawo magana a kasa.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto dazu cewa wasu daga cikin Gwamnonin Najeriya suna ta kokarin nesanta kansu daga zargin da shugaban kasa yake yi masu.

Gwamnonin Benuwai, Ebonyi, Kwara, Filato, Ogun da Ribas sun ce ba su cikin wadanda Muhammadu Buhari yake magana a kudin goron da ya yi.

Mai taimakawa Gwamnan Benuwai a yada labarai da hulda da jama’a, Terver Akase yace ko da wasu Gwamnonin na wannan aiki, ban da Samuel Ortom.

Kara karanta wannan

Wike Ya Rabu da Atiku da Ayu, Ya Koma Kan Gwamnoni 5, Ya Jefa Masu Kalubale

Ba da mu ba - Ortom, AbdulRazaq

Akase yake cewa Samuel Ortom yana cikin Gwamnonin farko da suka ba kananan hukumomi gashin kansu, don haka babu dalilin taba masu asusu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An rahoto Babban sakataren Gwamnatin AbdulRahman AbdulRazaq a Kwara, Rafiu Ajakaye yana cewa babu ruwan jiharsu da bayanin shugaban kasar.

Gwamnoni
Shugaba Buhari tare da wasu Gwamnoni Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Ajakaye ya nuna gwamnatin Kwara ba ta taba abin da kananan hukumomi suka mallaka.

Duniya ta shaidi Ebonyi Inji Chooks Oko

Irin wannan bayani ya fito daga bakin Chooks Oko a wani jawabi da ya fitar, yace a dalilin tsantsenin David Umahi, sai da jihar Ebonyi ta samu lambar yabo.

Hadimin Gwamnan yake cewa bankin Duniya ya bada kyaututtuka ga Gwamnatin David Umahi saboda yadda yake gaskiya wajen kula da dukiyar jiharsa.

Idan maganar Kwamishinan yada labarai na Filato, Dan Manjang gaskiya ce, Gwamna Simon Lalong bai cikin gwamnonin da shugaban kasa ya suka.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: FG Ta Gargadi Wasu Gwamnoni Kan Amfani Da Yan Daba A Lokacin Kamfe

Shi ma Kwamishinan labarai na jihar Ogun, Waheed Odusile yace ba su cin kudin kananan hukumomi.

Takwaransu a jihar Ribas, Chris Finebone yace Gwamna Nyesom Wike ya saki mara ga kananan hukumomi domin su kula da dawainiyar da ke kan wuyansu.

Jaridar ta nemi jin ta bakin sauran Gwamnoni masu-ci, amma ba a iya tuntubarsu ko hadimansu ba.

Baraka a Jam'iyyar LP

An samu rahoto shugabannin LP na reshen jihar Ogun sun bada sanarwar korar mutane 11 daga Jama’iyya, har da Darektan Kamfe na Peter Obi.

Ana zargin tsohon Hadimin shugabannin Najeriya Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, Doyin Okupe da rashin amana kan abin da ya shafi kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel