Ayarin Gwamnan Jihar Adamawa Sun Samu Hatsari, Mutane Sun Rasu

Ayarin Gwamnan Jihar Adamawa Sun Samu Hatsari, Mutane Sun Rasu

  • Wani hatsari mai muni ya rutsa da ayarin motocin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, yana hanyar zuwa Mubi
  • Bayanai sun ce motar 'yan bangan dake wa gwamna Rakiya ne hatsarin ya shafa, mutane huɗu daga ciki sun rasu
  • A karshen makon da ya gaba, wata Tifa ta murkushe motoci biyu daga cikin ayarin gwamnan

Adamawa - Rahoton da muke samu yanzu haka ya nuna cewa wasu Motocin dake cikin Ayarin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, sun yi hatsari.

Jaridar Punch ta tattaro cewa mutane hudu sun rasu a mummunan hatsarin wanda ya rutsa da motar Toyota Hilux ɗauke da 'Yan Banga dake wa gwamnan rakiya.

Gwamna Ahmadu Fintiri.
Ayarin Gwamnan Jihar Adamawa Sun Samu Hatsari, Mutane Sun Rasu Hoto: punchng
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya auku da Motar ne a Fadamareke, ƙaramar hukumar Hong, yayin da gwamnan ke kan hanyar zuwa garin Mubi domin halartar wani taron yakin neman zaɓe.

Kara karanta wannan

FG Tace Gwamnatocin Jihohi ne Suke kara Tsunduma ‘Yan Najeriya Cikin Matsanancin Talauci

An tattaro cewa tuni aka ɗauki gawarwakin waɗanda suka mutu, Bako Kaura, shugaban yan daban PDP, da wani mai suna Adamu, ɗa ga Kaura zuwa ɗakin aje gawa na Cibiyar lafiya ta tarayya (FMC), Hong.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan ragowar mutum biyar da suka ji raunuka an ɗauke su a Motar Ujila ta gidan gwamnati da wata Hilux domin kai su Asibiti a ci gaba da kulawa da lafiyarsu.

Likitan gwamna na kai da kai kuma shugaban Asibitin gidan gwamnatin Adamawa, Dakta William Teri, Ɗaya daga cikin waɗanda suka ba da agaji a wurin ya bi motocin da suka ɗauki majinyatan zuwa Asibiti.

Wata majiya, ɗaya daga cikin mutanen yankin da suka kai agaji ga waɗanda suka yi hatsarin ya ce:

"Mun ɗauki gawar mutane uku nan take amma akwai wani ɗaya da bana tunanin zai tashi saboda raunukan da ya ji sun yi muni. Kusan mutane 9 ne a cikin motar, shugaban 'yan Bangan Fintiri/Farauna na ciki."

Kara karanta wannan

Aminu Zai Gurfana Gaban Kotu a Yau Laraba Kan Zargin Cin Mutuncin Aisha Buhari

Gwamna Fintiri, wanda ya taimaka wajen ɗauke waɗanda hatsarin ya shafa, ya nuna damuwarsa da faruwar lamarin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Fintiri Ya Sha da Kyar Yayin da Babbar Mota Ta Murkushe Motocin Ayarinsa

A karshen makon da ya gabata mun kawo muku cewa wata Tifa ta murkushe motoci biyu a Ayarin gwamnan jihar Adamawa

Gwamna Ahmadu Fintiri ya shallake rijiya da baya yayin da wata Tifa ta murkushe motoci biyu daga cikin Ayarin motocinsa a Yola, Adamawa.

Wani Ganau yace motar wacce ta sha ƙarfin Direban ta tunkari Bus Marsandi da gwamna ke ciki Direban ya yi kokarin kaucewa, yan sanda biyu suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel