Tambuwal Ya Samu Babban Muƙami Daga Majalisar Dokokin Tarayya

Tambuwal Ya Samu Babban Muƙami Daga Majalisar Dokokin Tarayya

  • Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Dokokin Tarayya, NASC, a ranar Juma'a, 18 ga watan Nuwamba ta yi sauye-sauyen wasu mukamai
  • Daya daga cikin manyan nadin da hukumar ta yi a ranar Juma'a shine kara wa Sani Magaji Tambuwal girma zuwa Akawun Majalisar Tarayya (CNA)
  • Kafin nadinsa, Tambuwal shine sakatare na sashin kudin da asusu na Majalisar Tarayya

FCT, Abuja - Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Dokokin Tarayya, NASC, ta nada Sani Magaji Tambuwal mukamin Akawu na rikon kwarya ga Majalisar Tarayya (CNA).

Kafin nadin da aka masa a ranar Juma'a, 18 ga watan Nuwamba, Tambuwal ne sakatare na bangaren kudi da asusun na Majalisar Tarayya, The Nation ta rahoto.

majalisa
Tambuwal Ya Samu Babban Mukami Daga Majalisar Dokokin Tarayya. Hoto: @nassnigeria.
Asali: Twitter

An yi wa Tambuwal karin girma zuwa kujerar na CNA ne bayan murabus din Arc. Amos Olatude Ojo a ranar Talata, a ranar 15 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Ta Rangada Lalle na Musamman Mai Nuna 'Dan Takaranta a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran wadanda aka yi wa karin girman bayan Tambuwal

Hukumar ta kuma yi wa Ogunlana Kamoru karin girma daga sakataren harkokin sharia zuwa mataimakin CNA kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kari da haka, NASC ta yi wa Henrietta Aimua-Ehikioya karin girma daga (Sakataren Ayyuka Na Musamman) zuwa Sakataren Harkokin Shari'a.

An yi wa Birma Shuaibu karin girma daga sakataren, harkokin kula da mutane yayin da Umoru Barde Ali (Direkta Na Dakin Bada Magunguna) zuwa sakataren rikon kwarya na bincike da bayanai.

An nada Omogbehin Yomi (Direktan Ayyukan Majalisa) matsayin sakataren rikon na Ayyuka na musamman da Mr Inyang Clement Titus (Direkta Na Asusu) an nada shi matsayin sakataren bincike da bayanai.

Nwoba Andrew (Direktan Gudanarwa) an masa karin girma zuwa sakaren riko, na shirye-shirye da kasafin majalisa.

Banyi Nadamar Dakatar Da Tsige Shugaban Kasa Ba - Sanata Omo Agege

Kara karanta wannan

Bayan Rasa ‘Dan Majalisa, Mutuwa ta Sake Dauke Wani Na Hannun Daman Bola Tinubu

A bangare guda, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya ce baya nadamar hana majalisar dattawa ta tsige shugaban Muhammadu Buhari ba.

Omo-Agege, wanda ake zargi da kitsa harin da aka kai majalisar dattawa, ya isa harabar majalisar ne da wasu ‘yan daba da ake kyautata zaton suna yi masa aiki a ranar da za'a saurari kudirin.

Yayin da yake martani kan lamarin a ranar Alhamis yayin yakin neman zabensa a Asaba, dan takarar gwamnan jihar Delta na jam’iyyar APC, ya bayyana cewa bai taba yin nadamar matakin da ya dauka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel