Bayan Rasa ‘Dan Majalisa, Mutuwa ta Sake Dauke Wani Na Hannun Daman Bola Tinubu

Bayan Rasa ‘Dan Majalisa, Mutuwa ta Sake Dauke Wani Na Hannun Daman Bola Tinubu

  • Dr. Mueez Akande ya rasu yana da ‘dan shekara 72, Marigayin yana cikin masu kusanci da Bola Tinubu
  • A lokacin yana raye, Mueez Akande ya rike kujerar Kwamishinan kasuwanci a Gwamnatin jihar Legas
  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi wa iyalin Surukin na Bola Tinubu ta’aziyyar wannan babban rashi

London - Wani rahoto da aka samu daga This Day ya tabbatar da Mueez Akande wanda tsohon na-kusa da Bola Ahmed Tinubu ne, ya kwanta dama.

Mueez Akande mutumin Bola Ahmed Tinubu ne wanda suka yi tafiyar siyasa tare, har ya rike masa kwamishinan kasuwanci a lokacin yana Gwamna.

Mai dakin Akande ta tabbatar da mutuwar mai gidanta yana mai shekara 72 a Duniya.

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ta bakin Gboyega Akosile ya fitar da jawabi yana yi wa Miss Lola Akande da iyalinta ta’aziyyar mutuwar mijinta.

Kara karanta wannan

Yadda Gwmanan Jihar Ebonyi Ya Nuna Gyan Bayan Karara Ga Dan Takarar Jami'iyyar APC

Marigayin Suruki ne a wajen ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar APC, domin ‘danuwa ne ga mai dakinsa, Sanatar Legas ta tsakiya, Oluremi Tinubu.

Rahoton yace Akande Likita ne wanda daga baya ya fada harkar siyasa da kasuwanci a Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Asiwaju TInubu
Bola Tinubu da mutanensa Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Mutuwa biyu a makon nan

Likitan ya rasu ne kwanaki biyu bayan mutuwar Hon. Olayiwola Olawale, wani ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Mushin II a majalisar dokokin Legas.

Mutuwar Akande ta tsaiwaita wa’adin makokin da Bola Tinubu yake yi. A jiya ne aka birne Hon. Olawale a Legas bayan ya rasu a wajen taron APC a Jos.

Hakan ya na nufin a cikin sa’o’i 48, ‘dan siyasar ya rasa mutane biyu cikin na hannun daman shi.

Zargin harkar kwayoyi

Kwanakin baya Sahara Reporters ta rahoto ana zargin Adegboyega Mueez Akande da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi daga Amurka zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tona Masu Lallaban Shi Wajen Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Wata kungiya tace Akande ya taimaka wajen shigo da kwayoyi kasar nan tsakanin 1988 da 1992. Zuwa yanzu ba a san gaskiyar zargin wannan badakala ba.

Ana zargin Tinubu ya taba karbar $100, 000 daga wajen sa domin bude akawun a banki. A wani lokacin dabam kuma ya nuna bai da wata alaka da Akande.

APC za tayi amfani da manoma da ‘yan Kasuwa

Labari ya zo kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC zai yi amfani da manoma da ‘yan kasuwa domin ganin Bola Ahmed Tinubu ya yi galaba.

Sanata Gbemisola Ruqayyah Saraki tayi wannan bayani yayin da ta kaddamar da kwamitin kasuwanci a takarar APC a tsakiyar makon nan a garin Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel