Yadda Bidiyon Wani Ɗan Nigeria Ya Karaɗe Shafukan Sada Zumunta Bayan Ya Gayara Babur Ɗinsa

Yadda Bidiyon Wani Ɗan Nigeria Ya Karaɗe Shafukan Sada Zumunta Bayan Ya Gayara Babur Ɗinsa

  • Kirkira dai a Nigeria ba wani sabon abu bane, duba da yadda ake samun matasa a kasar na yawan yi.
  • Ana yawan samun matasa da suke kirkirar injina mashina da dai sauran abubuwan amafanin yau da kullum
  • A kwanan ma a jihar Barno an samu yaran da ya gina gadar saman Jihar da tabo

Akure: An ga wani dan Najeriya yana hawa babur na musamman wanda ke da sitiyari kamar mota. Matashin mai babur ɗin wanda ya fito daga Akuren jihar Ondo, an ganshi yana ta kewaye gari da babur dinsa. Baya ga samansa sitiyari kamar mota, babur din yana madannai a hannu wanda ake sarrafa shi da hannun maimakon kafa. Ana sarrafa babur ɗin da kafa maimakon hannu ba kamar yadda ake sarrafa babur ba. Shahrarren mai amfani da kafar nan ta Twitter, Segun Ariyoosu ne ya ɗauki hoton bidiyon wanda ya ja hankalin ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 Da Buhari Yayi Lokacin Mulkinsa Soja Kuma Yake Maimaitawa Yanzu, Shehu Sani

Mai Babur
Yadda Bidiyon Wani Ɗan Nigeria Ya Karaɗe Shafukan Sada Zumunta Bayan Ya Gayara Babur Ɗinsa Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

Martani daga masu amfani da Twitter ‘Yan Najeriya a shafin Twitter na yaba wa hazakar matashin. Mutane da yawa sun yi sha'awar sakon da suka yaba da kirkirarsa.

Ga kadan daga cikin abin da mutane ke cewa a kasa: @zynowles ya ce: "Kayi tunani sosai, wani lokacin yanayi kan taimakawa mutum musamman ma matashi mai irin wannan basirar amma ina? A Najeriya akwai matasa masu mafarkai, hangen nesa, hazaka da basira. indai za'a amfane su to za'a magance abubuwa da yawa" @momolesho said: Wannan Babur din kamata yai ace WW11 mai kayan aikin hannu. @ ShugabanR yayi sharhi: "Yan Najeriya suna da Basira."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon:

Yan Najeriya sun yaba wa mutumin da ya ƙera Tagogi Da Kofofi da Gilashi

A wani labarin makamancin haka, Legit.ng ta ruwaito cewa, wani mahayin Keke dan Najeriya ya ƙera ƙofofi da Tagogi na gilashi a Napep dinsa. Mutumin da ke sana’ar sa a garin Jos ta jihar Filato. An dauki hoton yadda yake aikinsa tare da yaɗa su a facebook da sauran shafukan kafafen sada zumunta. Yan Najeriya da dama sun yaba wa mutumin da ya inganta tare da gyara Napep dinsa dan ƙara yawan fasinjoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel