Muhimman Abubuwa Uku Da Suka Wakana A Gwamnatin Buhari A Lokacin Mulkin Soja Da Yanzu

Muhimman Abubuwa Uku Da Suka Wakana A Gwamnatin Buhari A Lokacin Mulkin Soja Da Yanzu

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dai ta kasance mai cike da dimbin al’amura tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015. Wasu daga cikin wadannan al’amura dai an bayyana su a matsayin wasu abubuwa da suke maimata kansu a zaman da yai na mulkin soja a 1983 zuwa 1985 da kuma yanzu da yake mulki kamar yadda tsohon dan majalisar dattawa, Shehu Sani ya yi ikirari Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a baya-bayan nan, ya bayyana wasu manyan abubuwa guda uku da suka faru a zamanin mulkin Buhari na 1983-1985 da kuma wannan gwamnatin ta sa ta yanzu.

Shugaba Buhari
Muhimman Abubuwa Uku Da Suka Wakana A Gwamnatin Buhari A Lokacin Mulkin Soja Da Yanzu Hoto: @BuhariSallau1
Asali: UGC

Kamar yadda ya fara da:

1. Rufe iyaka A shekarar 1984, gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Janar Muhammadu Buhari, ta rufe iyakokin Najeriya da dukkan kasashen da ke makwabtaka da ita a yankin ECOWAS (ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Tsakiya). Haka kuma, a watan Agustan 2019, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari ta bayar da umarnin rufe iyakokin Najeriya. Gwamnatin ta ce, rufewar, wata hanya ce ta hana shigo da muggan kwayoyi, makamai da kayayyakin amfanin gona zuwa Najeriya ba bisa ka'ida ba daga kasashen da ke makwabtaka a yankin Afirka ta Yamma. Wannan rufewar ta ɗauki sama da shekara guda lokacin da Gwamantin Tarayya ta ba da umarnin sake buɗe kan iyakokin ƙasa guda huɗu a cikin Disamba shekarar 2020. 2. Sake fasalin Naira Domin kawo karshen yadda ake bankado kudaden Najeriya da ake zargin gurbatattun ‘yan siyasar jamhuriya ta biyu ne, gwamnatin Janar Buhari ta sake fasalin kudin Najeriya a shekarar 1985. A matsayinsa na shugaban kasa a lokacin, Buhari ya ba da umarnin buga sabbin takardun kudi na Naira domin tunkarar kalubalen cin hanci da rashawa wanda yake zargin yai kasar katutu Hakazalika, a ranar 26 ga watan Oktoba, gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na sake fasalin kudin kasar (Naira). Emefiele a cikin sanarwarsa ya bayyana cewa, sake fasalin takardun na da nufin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki da kuma yaki da ayyukan masu aikata laifuka da ke taimakawa wajen samar da kudaden ayyukan ta'addanci a fadin kasar. A cewar gwamnan babban bankin na CBN , sabbin takardun kudi za su fara aiki ne daga ranar 15 ga watan Disamba, kuma duk tsofaffi da sabbin kudaden da ake da su za su ci gaba da kasancewa har zuwa ranar 31 ga watan Janairu. 3. Sankamo Dikko da Nnamdi Kanu Najeriya Dikko wanda ya rike mukamin ministan sufuri daga shekarar 1979 zuwa 1983, ya yi gudun hijira a Landan bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya hambarar da gwamnatin Shehu Shagari. Gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Janar Buhari (mai ritaya) ta zarge shi da laifin almundahanar miliyoyin daloli daga kudaden shigar man Najeriya a lokacin da yake rike da mukamin ministan sufuri. Ba da daɗewa ba, an gano shi a cikin akwati a filin jirgin sama na Stansted wanda ake da'awara jakar diflomasiyya ce a ranar 5 ga Yuli, 1984. Akwatin da aka ce ya nufi birnin Lagos na Najeriya, abin da mutane da yawa suka bayyana a matsayin garkuwa da gwamnati ta amince da shi wanda kuma gwamnatin Birtaniya ta dakile shi.

Kara karanta wannan

Luguden NAF Ya Halaka Manyan Yan Bindiga 3 da Ake Nema da Mayankansu a Jihohin Arewa

A ranar 30 ga watan Yuni, 2021, labari ya bazu cewa hukumomin Najeriya sun kama shugaban kungiyar IPOB a Kenya. Da yake magana game da kama shi, wani dan uwa ga shugaban kungiyar IPOB, Prince Kanu yayin da yake neman a yi wa Nnamdi adalci, ya ce gwamnatin Kenya da Najeriya sun yi wa dan uwansa hukunci da bai kamata ba kamar yadda yace a kalamansa:

" Sun keta ka'idoji mafi mahimmanci na tsarin shari'a, ture tsarin fasalin kasa da kasa na daya daga cikin manyan laifuffukan da zai sa wasu jihohi a Nigeria su aikata. Dole ne a hukunta Najeriya da Kenya. Ina neman a yi wa dan uwana Nnamdi Kanu adalci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karshe Buhari ya fadawa ‘yan Najeriya wadanda za su zaba a zaben shugaban kasa na 2023 An shawarci yan Najeriya da su tabbatar sun yi zabin da ya dace kuma su zabi duk wanda suke ganin ya dace a zaben 2023 mai zuwa. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar a ganawarsa da Sarki Charles III. A cewar shugaban, yana da kwarin gwiwar cewa mai rike da takarar jam'iyyar Bola Tinubu ne, zai lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel