Albashin Rabin Wata: Majalisar Zartarwar ASUU ta Shiga Ganawar Sirri

Albashin Rabin Wata: Majalisar Zartarwar ASUU ta Shiga Ganawar Sirri

  • Majalisar zartarwa ta kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’in Najeriya, ASUU, sun shiga ganawar sirri a yau Litinin a sakateriyar kungiyar
  • Ganawar sirrin na samun jagorancin shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke inda za a tattauna kan batun biyansu albashin rabin wata
  • Wata majiya daga majalisar zartarwa da ta bukaci a boye sunanta tace suna kammala taron zasu zanta da manema labarai kamar yadda suka saba

FCT, Abuja - Mambobin majalisar zartarwa ta kungiyar malaman jami’o’i masu koyarwa, ASUU, ta shiga ganawar gaggawa kamar yadda jaridar Daiy Trust ta rahoto.

ASUU ta shiga ganawar sirri
Albashin Rabin Wata: Majalisar Zartarwar ASUU ta Shiga Ganawar Sirri. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Taron sirrin da suka shIga sun fara shi ne wurin karfe 12:42 na yammacin Litinin kuma ana yin shi ne a sakateriyar kungiyar dake jami’ar Abuja.

Taron wanda yake samun jagorancin shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, zai mayar da hankali ne kan batun biyan albashin rabin wata da lakcarorin suka samu.

Kara karanta wannan

Shugaban Masu Rinjaye A Majalisar Wakilai Doguwa Ya Magantu Game Da Batun Sauya Shekarsa Daga APC

Wani mamba a majalisar zartarwar wanda yayi magana da Daily Trust tare da bukatar a adana sunansa yace za a zanta kan sauran matsalolin kuma za a yi jawabi ga manema labarai kamar yadda aka saba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lakcarori Zasu Sha Jar Miya, FG Ta Basu Albashin Rabin Wata

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta biya lakcarorin jami’a dake karkashin kungiyar malamai masu koyarwa ta ASUU albashin kwanaki 18 na watan Oktoba, Legit.ng Hausa ta tabbatar da hakan.

Lakcarori da dama da Legit.ng Hausa ta tuntuba sun tabbatar mata da hakan inda suka ce an biya su rabin albashinsu ne kuma yana nuna na watan Oktoba.

An rahoto yadda malaman jami’an suka koma yajin aikin watanni takwas da suka yi a ranar 14 ga watan Oktoban 2022. An yi kira ga lakcarorin da su koma bakin aiki a ranar da aka janye yajin aikin.

Kara karanta wannan

2023: Ƙarin Ciwan Kai Ga Atiku, Jam'iyyar APC Ta Ƙara Samun Gagarumin Goyon Baya Daga Wasu Jiga-Jigan PDP

A bayanin da wani malamin jami’a yayi wa Legit.ng Hausa, yace ya samu albashin babu zato balle tsammani duk da cewa ba wannan bace yarjejeniyar dake tsakaninsu da gwamnatin tarayya ba.

”Na samu Albashin wurin karfe shida na yammacin Alhamis, 3 ga watan Nuwamban 2022. Rabonmu da jin shigowar albashi tun a wata Fabrairu.
”Ba zan ce ina daukin kudin ba saboda tuni na gane cewa ba zan iya rayuwa a kan albashina ba. Shiyasa na kama wasu ayyukan tun kafin ma a tafi yajin aiki.“

Asali: Legit.ng

Online view pixel