Tashin Hankali Ga ’Yan Afrika Yayin da Wani Abon Nau’in Sauro Mai Sa Zazzabi Na Kaura Daga Asia Zuwa Afirka

Tashin Hankali Ga ’Yan Afrika Yayin da Wani Abon Nau’in Sauro Mai Sa Zazzabi Na Kaura Daga Asia Zuwa Afirka

  • Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiwuwar a samu mummunan barkewar zazzabin cizon sauro a Afrika
  • An samu wani sabon nau'in sauro daga Asiya da ya kutso zuwa nahiyar Afrika, ya fara aikata barna a yankuna da dama
  • Ana fargabar karuwar yaduwarsa zai kai ga illata mutane sama da miliyan 30 a Afrika, babban barazana ga lafiya

Afrika - Akwai yiwuwar mazauna nahiyar Afrika su fara fuskantar zazzabin cizon sauro mai tsananin yayin da wani nau'in sauro da ake kyautata zaton dan yankin Asiya ne ya fara yawo a Afrika.

A cewar masana, wannan lamari na barkewar sabon nau'in zazzabin cizon sauro a Afrika zai fi shafar mazauna birni ne, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Sabon nau'in saura ya fara yawo a Afrika, jama'a sun fara maleriya
Tashin Hankali Ga ’Yan Afrika Yayin da Wani Abon Nau’in Sauro Mai Sa Zazzabi Na Kaura Daga Asia Zuwa Afirka | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yaya bantun magance wannan matsala?

A bangaren magani, masanan sun ce wannan nau'i dai na zazzabi ba lallai ya kau ta hanyar amfani da magunguna na yau da kullum da ake aiki dasu a nahiyar ta Afrika ba.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni daga Djibouti da Ethiopia sun bayyana cewa, an fara ganin karuwar yawan kamuwa da cutar maleriya a yankin, kuma kwaje-kwaje sun nuna tushen cutar daga cizon wancan sauro dan Asiya, rahoton South China Morning Post.

Wacce barazana ake iya fuskanta nan gaba?

Da suke tsokaci game da abin da zai iya faruwa gaba, masana sun bayyana cewa, ci gaba da yaduwar wannan nau'i na sauro a Afrika zai iya jawo mummunar barazana ga rayukan 'yan Afrika akalla miliyan 30.

Rahotannin kiwon lafiya sun sha bayyana cewa, nahiyar Afrika ne kan gaba wajen samun mace-mace ta sanadiyyar cizon sauro, wanda barazana ce da har yanzu ba a iya magancewa ba.

Hakazalika, an ce akasarin tushen wannan matsala ta yawaitar yaduwar sauro ya fi yawa a karkara a Afrika, sabanin yadda aka naqalto na wannan sabon nau'in sauron Asiya.

Kara karanta wannan

Daruruwan Fusatattun Matasa Sun Rufe Babban Hanyar Bauchi-Tafawa Ɓalewa

Zazzabin cizon sauro yana kashe yan Najeriya 9 a kowane minti 60, Minista

A wani labarin, ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya koka kan yadda ake samun karuwar mace-mace da ciwon dake da alaƙa da zazzabin cizon sauro a faɗin kasar nan.

Dailytrust ta ruwaito ministan ya kara da cewa yan Najeriya 9 ne suke mutuwa da ciwon a kowace awa ɗaya.

Ehanire ya bayyana hakane ranar Litinin a Abeokuta, yayin da tawagar ma'aikatar lafiya da kuma kungiyar taimakon lafiya (SFH) suka ziyarci mataimakiyar gwamnan Ogun, Mrs. Noimot Salako-Oyedele.

Asali: Legit.ng

Online view pixel