Karin bayani: Gwamnonin Kudu Sun Shiga Ganawa Kan Yadda Za a Sako Nnamdi Kanu

Karin bayani: Gwamnonin Kudu Sun Shiga Ganawa Kan Yadda Za a Sako Nnamdi Kanu

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, gwamnoni a yankin kudancin Najeriya sun shiga wata ganawar sirri
  • Ana kyautata zaton za su tattauna ne kam lamurran da suka shafi tsaro da lamuran yankinsu da zaman lafiya
  • Hakazalika, an ce za su tattauna kan lamarin da za ya shafi ci gaba da tsare Nnamdi Kanu, shugaban 'yan IPOB

Jihar Enugu - Gwamnonin Ebonyi, Enugu da Abia da mataimakin gwamnan Anambra da Imo sun shiga wata ganawar sirri a gidan gwamnatin jihar Enugu, Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi wanda kuma shine shugaban gwamnonin Kudu maso Gabas ne ke jagorantar zaman na gwamnoni da mataimakansu.

Ana kyautata zaton cewa, daya daga abin da za a tattauna a zaman ya hada batun shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

Gwamnonin Kudu za su tattauna kan batun Nnamdi Kanu
Yanzu-Yanzu: Gwamnonin Kudu Sun Shiga Ganawa Kan Yadda Za a Sako Nnamdi Kanu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hakazalika, an ce za su tattauna kan lamarin da ya shafi tsaron yankin, tare da nemo mafita ga matsalolin tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan baku manta ba, a kwanakin da suka gabata ne aka sace wasu mutane 30 kusa da titin Enugu zuwa Nsukka, ciki har da hadimin gwamna da dalibai.

A bangaren Nnamdi Kanu, an tsare shi tare da gurfanar dashi a gaban kotu tun shekarar da ta gabata.

Kotu ta ba da umarnin a sake shi, amma hukumomin gwamnati na ci gaba da bincike kan lamarinsa tare da bayyana dage kara.

Wadanda suka halarci zaman

Daga cikin wadanda suka halarci zaman sun hada da gwamna Rt. Hon. Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da David Umahi na jihar Ebonyi, rahoton Daily Post.

Hakazalika da Prof. Charles Soludo na jihar Anambra da Hope Uzodinma na jihar Imo. Wadannan gwamnoni biyu sun samu wakilcin mataimakansu ne; Dr. Onyekachukwu Ibezi da Prof. Placid Njoku.

Kara karanta wannan

Babu Uban Da Zai Tsigeni Daga Kujerar Shugaban PDP, Iyorcia Ayu Ya Fusata

Buhari Yayi Magana Akan Batutuwan Tsaro da Amurka, Burtaniya da Sauransu Ke Yi Kan Abuja

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bukaci 'yan Najeriya da su kwantar da hankala, amma su kasance a ankare kan shawarwarin tsaro da kasashen turai suka fara bayarwa kan birnin tarayya Abuja.

A cewar wata sanarwa da Buhari ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya shawarci 'yan kasa da jami'an tsaro da su zama masu sanya ido kan lamarin tsaron kasar nan.

Idan baku manta ba, a makon nan ne kasar Amurka ta ba 'ya'yanta shawarin fara barin Najeriya sakamakon tsoron barazanar tsaro da ka iya biyo baya a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.