Babu Uban Da Zai Tsigeni Daga Kujerar Shugaban PDP, Iyorcia Ayu Ya Fusata

Babu Uban Da Zai Tsigeni Daga Kujerar Shugaban PDP, Iyorcia Ayu Ya Fusata

Shugaba uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Iyorchia Ayu, ya tabbatarwa al'ummar kauyensa cewa babu wanda zai cireshi daga kujerarsa.

Ayu ya bayyana hakan ne yayin jawabi da al'ummar kabilar Jembga a gidansa dake garin Gboko, jihar Benue, rahoton DailyTrust.

Yace su kwantar da hankulansu babu abinda zai faru da shi yana nan daram dam kan kujerarsa kuma ba zai yi murabus ba.

Iyorchia
Babu Uban Da Zai Tsigeni Daga Kujerar Shugaban PDP, Iyorcia Ayu Ya Fusata
Asali: Twitter

Yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"PDP tsintsiya ce madaurinki daya. Ina kokarin gann ban kunyata al'ummar Benue ba da kuma yan Najeriya gaba daya."
Idan kuka samu labarin cewa sun son tsige Ay daga kujerar shugaban jam'iyya, ku kwantar da hankulanmu; babu wanda zai koreni daga kujerar shugaban jam'iyyarmu."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

"Zan sauka ranar da Allah yayi."
"Allah ya kare ni har lokacin da na tafi Turai jinya, Allah ya kareni."

Asali: Legit.ng

Online view pixel