Gargadin Kai Hari: Shin Da Gaske An Dasa Bama-Bamai A Abuja? An Samu Bayanai

Gargadin Kai Hari: Shin Da Gaske An Dasa Bama-Bamai A Abuja? An Samu Bayanai

  • Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa rahoton cewa an dasa bama-bamai a fadin Abuja ba gaskiya bane
  • Olumuyiwa Adejobi, kakakin hukumar ya yi Alla-wadai da wasu shahrarru da akewa kallon mutanen kirki amma suna yada labarun karya
  • Adejobi ya bayyana cewa mazauna birnin tarayya su kwantar da hankulansu babu wani hari da za'a kai

FCT, Abuja - Hukumar yan sandan Najeriya ta yi watsi da labaran cewa an dasa bama-bamai a wasu wurare dake birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Hukumar ta ce karya ne kuma da ban mamaki wasu da ake yiwa kallon mutanen kirki ke yada wannan labari.

Adejobi
Gargadin Kai Hari: Shin Da Gaska An Dasa Bama-Bamai A Abuja? Bayanai Sun Bayyana Hoto: OluMiuywa Adejobi
Asali: UGC

Hakan na kunshe cikin jawabin da Kakakin hukumar yan sandan kasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

Yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ban tunanin zamu yiwa kasarsu adalci idan muka cigaba da yada labarun karya don tada hankulan mutane da mazauna birnin tarayya da Najeriya gaba daya."
"Da ban mamaki da ban haushi ka karanta a labarai da soshiyar midiya cewa an dasa bama-bamai a dukkan unguwannin Abuja, har daga bakin wasu da ake yiwa kallon jakadun zaman lafiya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel