Shugaba Buhari Ya Taya Minista Pantami Murnar CIka Shekaru 50 A Duniya

Shugaba Buhari Ya Taya Minista Pantami Murnar CIka Shekaru 50 A Duniya

  • Shugaba Buhari ya ce sam bai yi zaben tumun-dare ba yayinda ya baiwa Malam Isa Ali Pantami mukami a gwamnatinsa
  • Ya siffanta Pantami matsayin matashi mai jajircewa wajen gudanar da aikinsa tsakani da Allah
  • Farfesa Isa Pantami zai cika shekaru 50 da haihuwa a ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, murnar cika shekaru hamsin cir a duniya.

Buhari ya bayyana cewa Malam Pantami na daya daga cikin ma'aikata mafi kwazo, jajircewa da amfani a gwamnatinsa.

Buhari-Pantami
Shugaba Buhari Ya Taya Minista Pantami Murnar CIka Shekaru 50 A Duniya Hoto: Presidency
Asali: Twitter

A jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ce zaben Pantami na daya daga cikin shawari mafi amfani da yayi a rayuwarsa, rahoton TheNation.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Isa Pantami zai cika shekaru 50 da haihuwa a ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba, 2022.

Buhari yace:

"Nadin Pantami na daya daga cikin zabi mafi alkhairi da nayi saboda ya bada gudunmuwa matuka ga mulkin kwarai."
"Pantami na da ilmin abubuwa masu zurfi kuma abin a yaba ne. Hakazalika yadda yake mayar da hankali kan aikinsa abin kwaikwaya ne."
"Yayinda ya cika wadannan shekaru na rayuwarka, ina rokon Allah ya cigaba da yi maka albarka tare isasshen lafiya da hikima don bautawa kasarka da al'umma."

An Ware Sheikh Isa Pantami Shi Kadai, An ba shi Kyautar Kasar Waje a Birnin Dubai

A baya mun kawo muku cewa Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu lambar yabo saboda kokarin da yake yi a ofis.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Ba Zasu Fahimci Alherin Buhari Ba Sai Daga Baya, Tinubu

Kamar yadda ya bayyana a Twitter a ranar Talata, 11 ga watan Oktoba 2022, Mai girma Ministan ya tashi da kyautar DWTC a Dubai a kasar UAE.

An ba Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami wannan lambar yabo ne la’akari da ayyukan da yake yi wa Najeriya tun da ya zama Ministan sadarwa a 2019.

Jaridar Science Nigeria tace an karrama Isa Pantami bayan ya gabatar da jawabinsa a game da yadda za a tafi da kowa a harkar sadarwa na zamani.

Pantami ya yi jawabin ne a taron GITEX wanda ake yi yanzu haka a dunkullaliyar kasar Larabawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel