Yan Najeriya Ba Zasu Fahimci Alherin Buhari Ba Sai Daga Baya, Tinubu

Yan Najeriya Ba Zasu Fahimci Alherin Buhari Ba Sai Daga Baya, Tinubu

  • Da Sannu Yan Najeriya Zasu Fahimci Irin Namijin Kokarin da Shugaba Buhari yayi, cewar Tinubu
  • Tinubu ya ce Shugaba Buhari ya gaji matsaloli da dama daga wajen gwamnatin da ta shude
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi dai ya cika alkawuran da ya yiwa al'ummar Najeriya

Abuja - Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, a ranar Talata ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari bisa kokarin da ya yiwa al'ummar Najeriya.

Tinubu ya ce Buhari ya kwantar da hankalinsa, da sannu yan Najeriya zasu fahimci darajarsa.

Tinubu ya bayyana hakan a jawabin da yayi na fatan alheri ga Buhari a taron bitar ayyukan Ministoci da Sakatarorin din-din-din dake gudana a Abuja, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

Tinub
Yan Najeriya Ba Zasu Fahimci Alherin Buhari Ba Sai Daga Baya, Tinubu Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Dan takaran yace ya kamata yan Najeriya su fahimci cewa Buhari ya tarar da matsalar tsaro da rashawa lokacin da ya karbi mulki daga wajen Jonathan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabin da hadiminsa Tunde Rahaman ya fitar, ya ruwaito Tinubu da cewa:

"A yanzu ba za'a yabawa kokari da wahalar da ya (Buhari) sha ba. Amma da sannu za'a fahimci irin namijin gudunmuwar da ya bada."
"Gwamnatin nan ta gaji matsaloli da dama. Daga baya ka (Buhari) fuskanci matsalolin da ba'a tsamanni kuma suka sake rikirkita lamura. Cutar Korona ta girgiza tattalin arzikin duninya, farashin danyen mai ya sauka hakazalika kudaden shiganmu."
"Ka yi kokari kuma ka jajirce kuma ya samu nasarori da yawa."

Na Cika Alkawuran Da Na Yiwa Yan Najeriya Cikin Shekaru 7, Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron bita kan ayyukan da Ministocinsa sukayi cikin shekaru 7 da suka gabata tun da ya hau mulki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu Sabbin Hotuna Daga Aso Villa Sun Nuna Tinubu Na Kus-Kus da Mataimakin Buhari

Buhari ya bayyana cewa lallai ko shakka babu ya cika dukkan alkawuran da ya yiwa al'ummar Najeriya.

Taron ya samu halartan tsohon shugaban kasar Kenya, Uhurru Kenyatta, rahoton Leadership.

Shugaban kasan ya bayyana irin nasarorin da ya samu a bangaren aikin noma, gine-gine, tsaro, kiwon lafiya, yaki da rashawa, dss.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel