Mace Ba Yar Goyo Bace: Bakano Ya Je Shagalin Auren Aminsa, Ya Gano Budurwarsa Ce Amaryar

Mace Ba Yar Goyo Bace: Bakano Ya Je Shagalin Auren Aminsa, Ya Gano Budurwarsa Ce Amaryar

  • Wani matashi dan Najeriya ya shiga dimuwa bayan ya halarci shagalin bikin amininsa a jihar Kano
  • A wajen taron, sai ya gano cewa amaryar budurwarsa ce ta ya shafe tsawon shekaru uku yana soyayya da ita
  • A cewar abokin mutumin, niyansa shine ya angwance da wannan budurwa

Wani matashi dan Najeriya ya shawarci masu amfani da shafukan soshiyal midiya da kada su taba yarda da mace yayin da ya bayyana yadda budurwa tayi rugu-rugu da zuciyar abokinsa.

Sambo Mai Hula ta shafinsa na twitter mai suna @Abdullahiabba_ ya bayyana cewa abokinsa ya halarci shagalin bikin auren wani aminsa a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba.

Mutane na rawa
Kada Ka Taba Yarda Da Mace: Bakano Ya Je Shagalin Auren Aminsa, Ya Gano Budurwarsa Ce Amaryar Hoto: Roberto Westbrook
Asali: Getty Images

Ga mamakin abokin Sambo, sai yaga cewa amaryar ba kowa bace face wata budurwa mai suna Fatima wacce ya shafe tsawon shekaru uku suna soyayya.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Sheke Mahaifinsa Har Lahira Bayan Ya Rafka Maka Itace

A zahirin gaskiya abokin Sambo ya so angwancewa da yarinyar amma sam mafarkinsa bai zama gaskiya ba don ya hadu da tangarda.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mata zasu baka kunya a kodayaushe. Wannan gayen ya shafe tsawon shekaru uku yana soyayya da Fatima da nufin aurenta a matsayin matarsa kwatsam sai ya halarci bikin amininsa a jiya sannan ya ga cewa Fatima ce amaryar.
“Kada ka taba yarda da mace,” Sambo ya rubuta.

Sambo wanda ainahin sunansa Abdullagi Abba Sambo ya tabbatar da faruwar lamarin ga Legit.ng.

Dan kasuwar ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a karamar hukumar Ungoggo da ke Kano.

Kalli wallafarsa a kasa:

Jama’a sun yi martani

@DoubleDeeZ_umar ya ce:

“Kada ka yarda da mace a wajen gidanku ko har a cikin gidanku?
“Kuma mai yake yi tsawon shekaru 3, yana bata mata lokaci?

Kara karanta wannan

"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Dan Jarida Makaho Yayi Tsokaci Kan Aure da rayuwarsa

“Wanda yake yi da gaske shine ya aureta.”

@Taste_made_oven ta ce:

“Niyan shekaru 3 kuma ana ta niya? Kana so ta jira har tsawon shekaru 9 ko me? Kada ka ga laifin Fatima dan Allah, ka daura laifin kan gayen da ya ajiyeta tsawon wannan lokaci yana jiran tsammani. Za mu iya magana kan aminin da ya nuna nufinsa karara.”

@Lefter_11 ya ce:

“Na taba soyayya da wata Fatima tun lokacin da take JSS 2 har SS3 ta kare da auren wani da ta hadu da shi kasa da shekara daya, dama Fatima sun iya karya zukata.”

Na Fasa Auren: Budurwa Ta Saka Zoben Baikonta a Kasuwa, Zata Siyar N8m

A wani labarin, wata matashiyar budurwa da ta soke aurenta ta saka zoben baikonta da farashin shi ya kai naira miliyan 10.2 a kasuwa.

Bayan ya bayyana karara ba yin auren za a yi ba, sai ta garzaya shafin Facebook domin tallata tsadadden zabon sumfurin Tifanny.

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka Cikin Dare Kusa Da Dakin Hotel

Ta saka farashin zoben na lu’u-lu’u kan $18,500, wanda yayi daidai da naira miliyan 8 wanda yayi kasa da farashin yadda aka siye shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel